Wata mata daga Jihar Florida a Amurka ta karbi lambar yabo ta Kundin Tarihi na Duniya (Guinness World Record) a ranar cikarta shekara 100, saboda kasancewa wadda ta fi tsufa a duniya.
Matar mai suna Edith Murway-Traina, ta cika shekara 100 a ranar Lahadin makon jiya.
Tun tana da shekara 98 da kwana 94 a lokacin da ta shiga gasa ta karshe ta daga nauyi a shekarar 2019.
Hakan ya ba ta damar samun lambar kasancewa mace mafi tsufa a cikin mata masu gasar daga karfe mai nauyi.
Murway-Traina za ta sake shiga wata gasar da za ta sake daga darajarta, kamar yadda aka shirya bayan farkon bullar cutar Coronavirus a watan Nuwamba.
Ta shafe shekaru a matsayin mai koyar da rawa kafin kawarta Carmen Gutworth mai shekara 91 ta gayyace ta wajen wata mai gasar rawa don ta kasance tare da ita a dakin motsa jiki.
“Yayin da nake kallon wadansu matan suna ta motsa jikinsu, na yi tunanin ni ma ya kamata in daura damara, in shiga cikin masu motsa jikin.
“Kuma a haka na fara yi har na fara iya shiga gasar da na yi bajinta da kalubalantar masu gasar.
“Daga nan na kai matsayin samun lambar Kundin Tarihi na Duniya.
“Bayan tafiya ta fara nisa, na gano cewa, ina jin dadin kasancewa a cikin masu motsa jikin, kuma ina kalubalantar kaina don in dan samu wani nau’in motsa jiki, kuma na inganta rayuwata.
“Ba da dadewa ba, na kasance cikin kungiyar masu gasar,” inji ta.
Murway-Traina ta daga karfe mai nauyin kilo 40 zuwa 150 a gasar da ta shiga, wadda ta sa ta lashe kofuna da yawa.
“A matsayina na mai wasan kwaikwayo kuma mai gasar rawa, na kasance koyaushe ina daukar wannan motsa jiki da muhimmanci a wani bangaren nishadantarwa.
“Tun lokacin da mutane suka gano ina da shekara 80 kuma ina yin wadannan abubuwa, sai hakan ya sa na zama sananniya.
“Jama’a suka fara mai da hankali sosai a kaina,” inji Murway-Traina.