Wani mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, Olufemi Ajadi Oguntoyin, ya janye daga takararsa, inda ya goyi bayan jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Da ya ke jawabi a wani taron da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a ranar Alhamis, Oguntoyin, ya ce ya janye takararsa ne domin mara wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso baya a takarar ta Shugaban Kasa.
- Sama da daliget 300 sun kira ni suna ikirarin ni suka zaba — Shehu Sani
- Zargin batanci: Rashin lafiyar Alkali ta janyo tsaiko a shari’ar Sheikh Abduljabbar
“Ni Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, bayan da na yi la’akari da abubuwa da yawa, kuma bisa maslahar babbar jam’iyyarmu da kasarmu, a yau na janye burina na tsayawa takarar Shugaban Kasa na goyi bayan takarar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
“Na yi alkawarin yin biyayya a kowane lokaci don yin hidima ga jam’iyyarmu da kasarmu,” inji shi.
Jam’iyyar NNPP dai na ci gaba da samun tagomashi, inda ’yan siyasa ke sauya sheka zuwa cikinta.