Mai kwacen wayan nan da mota ta buge shi a Kano ya mutu, a cewar rundunar ’yan sandan jihar.
A safiyar nan ta Talata ce mai kwacen wayan ya ce ga garinku nan a inda aka kwantar da shi, “a Asibitin Murtala,” inji kakakin rundunar, Abdullahi Harun Kiyawa, ya sanar.
Aminiya ta ruwaito ranar Lahadi cewa mota ta mai kwacen wayan ne a lokacin yake kokarin tserewa bayan ya yi wa wata mata fashin wayarta.
Kakakin ’yan sandan jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce mota ta kade shi ne a yayin da yake kokarin tsallaka titi bayan ya yi fashin.
- Mai kwace waya ya guntule yatsun matashi a Abuja
- Na kashe mutum 3, na caka wa 25 makami —Dan shekara 16 mai kwacen waya
A jiya, Kiyawa ya sanar cewa, “Bayan mun kai shi asibiti yana dan motsi, kashin bayansa ya karye (Spinal Code) kuma kansa ya fashe. Suna shawara su sa shi a “ICU”.”
Kwacen waya na daga cikin matsalolin tsaro da suka addabi jihar Kano, inda a wasu lokuta masu kwacen ka hallaka jama’a.
A sanadiyyar wannan matsala, gomman mutane a jihar sun rasa rayuwarsu a hannun masu kwace waya, wasa da dama kuma suka tsallake rijiya da baya da rauni ko asarar dukiya.