✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai kudin duniya Jeff Bezos ya ajiye aiki

Bezos yana da tarin dukiya da ta haura Dala biliyan 200.

Hamshakin attajirin nan dan kasar Amurka, Jeff Bezos, ya ajiye aikinsa na shugabancin kamfanin Amazon da ke hada-hadar kayayyaki ta Intanet.

A yau Litinin Andy Jassy zai maye gurbin Bezos, wanda ya kawo karshen zama shugaban kamfanin da ya shafe fiye da shekaru 20 yana jagorancinsa.

A shekarar 1994 Bezos ya kirkiri kamfanin na Amazon, inda ya fara sayar da littafai kafin ya habaka zuwa sayar da kayayyaki ta yanar gizo.

A yanzu alkaluma sun nuna kamfanin yana da darajar da ta haura Dala Tiriliyan 1.75.

Kamfanin ya samu riba mai tarin yawa a lokacin annobar Coronavirus, fiye da wacce ya samu a tarihi kasancewar mutane da dama na da bukatar kayayyaki da kuma ayyukan kamfanin.

Mujallar Forbes da ke fidda da alkaluma kan ababen da suka shafi rayuwar duniya, ta ce Bezos yana da dukiya da ta haura Dala biliyan 200.

Kafar labarai ta CNN ta ruwaito cewa, tun a watan Fabrairun da ya gabata ne kamfanin ya sanar cewa Bezos zai sauka daga mukaminsa.

Sai dai bayanai sun ce zai ci gaba da kasancewa yana da iko mai karfi a kansa.

Rabuwa da matarsa

A shekarar 2019 ce Bezos ya saki matarsa, MacKenzie Scott, bayan sun shafe tsawon shekara 25 suna tare.

A bisa wata al’ada da ba kasafai ake samunta a nan ba sai a kasashen Yammacin duniya, Jeff ya bai wa matar Dala biliyan 38 yayin rabuwarsu.

Yanzu MacKenzie ita ce ta uku a jerin mata mafiya arziki a duniya, kuma kimar kadarorinta ta kai Dala biliyan 6.1.

Tafiya duniyar wata

Bezos zai je duniyar wata a cikin kumbon farko mai dauke da mutane da dama wanda kamfaninsa na Blue Origin ya kera.

Bulaguron an tsara yin sa ne ranar 20 ga watan Yuli, kwana 15 kafin Jeff Bezos ya sauka daga mukamin Shugaban Kamfanin Amazon.

Kamfanin Blue Origin ya ce kanin attajirin, Mark Bezos, shi ma zai shiga ayarin wan nasa zuwa duniyar watan a cikin kumbon mai suna New Shepard.

Bezos mai shekara 57, ya wallafa shafin Instagram cewa, “Tun ina dan shekara biyar nake mafarkin tafiya zuwa duniyar wata.

“A ranar 20 ga watan Yuli, zan yi wannan babban bulaguron tare da kanina kuma babban aminina.”