Sarkin Kanuri na Legas, Mai Kanuribe Mustapha Muhammad ya rasu tare da ’yan uwansa biyu a wani hatsarin mota a kan hanyar Maiduguri zuwa Mafa a Jihar ta Borno.
Da take sanar da rasuwar tasa a ranar Talata, Gwamnatin Borno ta karyata labarin da ke yawo cewa Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum ya yi hatsarin mota a ranar.
- Mayakan Boko Haram sun kai hari Geidam
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
- Wanda ya jagoranci sace Daliban Kankara ya mika wuya
- Sheikh Gumi ya yi wa El-Rufai raddi kan ’yan bindiga
Kakakin Gwamna Zulum, Isa Gusau ya ce, “Labarin da wata kafar yada labarai da kasar waje ta yi cewa tawagar motocin gwamnan ta yi hatsarin moata ba daidai ba ne.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Cikin juyayi da tausayawa da girmamawa ga iyalansu, ina sanar da rasuwar Mai Kanuribe na Legas, Alhaji Mustapha Muhammad tare da ’yan uwansa biyu a hatsarin mota a kan hanyar Maiduguri zuwa Mafa ranar Talata a Jihar Borno.
“Amma kuma ina karin bayani da cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ba ya cikin wadanda suka yi hatsari, don haka rahoton da aka bayar ga gaskiya ba ne.”
Isa Gusau ya ce Mai Kanuriba ya ziyarci garin Mafa ne don nuna goyon baya ga Gwamnatin Zulum da jami’iyyar APC, amma ya riga gwamnan baro garin zuwa Maiduguri.
“Bayan tahowar Gwamna tare da Sanata Kashim Shettima da sauran shugabanni ne suka iske hatsarin da ya ritsa da basaraken a hanyarsu ta komawa daga Mafa.
“Daga nan ne Gwamna da sauran ’yan tawagar suka dauko gawarwakin zuwa gidajen iyalan mamatan a Maiduguri inda suka kuma yi musu ta’aziyya aka kuma yi janaza.”
Sanarwar rasuwar ta ce Gwamnan ya kadu matuka da rasuwar basaraken da sauran wadanda hatsarin motar ya yi ajalinsu.
Zulum “ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa Mai da wadanda suka rasu tare da shi, Ya sa su a Aljanna Firdaus,” inji sanarwar.