✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai Kaltungo ya zama shugaban kungiyar agaji ta JNI ta Jihar Gombe

A ranar Litinin da ta gabata ne kungiyar agaji ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Gombe ta tabbatar wa Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad…

 ‘Yan agajin Kungiyar Jama’atu a lokacin da suke fareti a Gombe.A ranar Litinin da ta gabata ne kungiyar agaji ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Gombe ta tabbatar wa Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad shugabancin kungiyar reshen jihar.
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamnan Jihar, Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, cewa ya yi a kasar nan kowa ya san aikin kungiyar ’yan agaji ta Jama’atu da yadda suke gudanar da aikinsu.
Gwamna dankwambo, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abubakar Sule Bage, ya ce zai ci gaba da ba kungiyar duk gudunmawar da ta dace.
Ya yi kira ga shugabanin kungiyar su ci gaba da wayar da kan mambobinsu don a samu dauwamammen zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
“Na san suna neman tallafi domin suna yin iya kokarinsu wajen ba da gudumawa ga jama’a a lokuta daban-daban musammam a lokacin aikin Hajji a filin jirgin sama don taimaka wa maniyyata,” inji Gwamnan.
Ya ba da gudunmawar Naira miliyan 10 ga gidauniyar kungiyar agajin don ci gaba da koya wa ‘yan agajin dabarun aiki.
Babban Daraktan ’yan agajin na kasa Alhaji Muhammad Ali Kaita, Shettiman Katsina, ya ce kungiyar agajin ta kafu ne a1959, a Jihar Gombe kuma an kafa ta a 1976.
Shettiman na Katsina, ya manufar kafa kungiyar agaji ita ce don taimaka wa Musulmi da wadanda ba Musulmi ba.
Sai ya bukaci ’yan agajin kungiyar Izala da na Fityanul Islam da Jundunlahi su kaunaci juna domin dukkansu aikin taimakon jama’a suke yi.
Da yake jawabi godiya jim kadan da tabbatar masa da wannan matsayi Mai Kaltungo, Injiniya Sale Muhammad, gode wa jama’ar da suka ba da gudumawarsu ga kungiyar  ya yi.
Ya gode wa Sarkin Bai na Gombe Jakada Ibrahim Yerima Abdullahi, kan yadda ya sadaukar da lokacinsa ya shugabanci taron.
Daga nan sai ya yi alkawarin sauke nauyin da aka dora masa yadda ya kamata tare da yin kira ga mambobin kungiyar su ba shi hadin kai da goyon baya.
Taron ya gudana ne a kofar fadar Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Shehu Abubakar, ya kuma samu halartar Wazirin Katsina Alhaji Muhammad Sani Lugga wanda ya wakilci Sarkin tare da Hakimin Dala Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran manya mutane daga sassan kasar nan.