✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai goyon bayan Isra’ila ya kai wa Isco hari da wuka

Kimanin mutum shida ne ciki har da wani matashi da ke dauke da wuka suka mamaye filin wasa a Jerusalam jim kadan bayan an kammala…

Kimanin mutum shida ne ciki har da wani matashi da ke dauke da wuka suka mamaye filin wasa a Jerusalam jim kadan bayan an kammala wasa a tsakanin Sifen da Isra’ila na neman gurbin tafiya Gasar Cin Kofin Duniya a Rasha a badi.

Matasan da ake kyautata zaton masu goya wa kulob din Isra’ila baya ne sun harzuka ne bayan Sifen ta bi Isra’ila har gida kuma ta doke ta da ci daya mai ban haushi doke kulob dinsu da ci daya mai ban haushi a ranar Litinin da ta wuce.  Hakan ta sa jim kadan bayan an tashi wasan sai wasu daga cikin magoya bayan Isra’ila suka mamaye filin wasan don nuna fushinsu a kan sakamakon wasan inda daya daga ciki ya nufi dan kwallon Sifen Isco da nufin ya yi masa illa.  Sai dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba inda jami’an tsaron suka yi nasarar damke shi kafin ya yi isa ga dan kwallon. 

Sai dai wata jarida a Isra’ila ta karyata batun cewa matashin yana dauke ne da wuka ba kamar yadda jaridun Sifen suka ruruta labarin cewa matashin yana dauke ne da wuka a lokacin da ya shiga filin wasan.

Yanzu dai Hukumar FIFA za ta gudanar da bincike, idan ta samu Isra’ila da laifi to za ta fuskanci hukunci.