✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai Garin da aka sace a Katsina ya kubuta

Rahotanni sun tabbatar da cewa Mai Garin Radda na Karamar Hukumar Charanci a Jihar Katsina, Alhaji Kabir Umar, ya shaki iskar ’yanci bayan ya kubuta…

Rahotanni sun tabbatar da cewa Mai Garin Radda na Karamar Hukumar Charanci a Jihar Katsina, Alhaji Kabir Umar, ya shaki iskar ’yanci bayan ya kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

A makon jiya ne Aminiya ta ruwaito cewa, Alhaji Kabiru ya fada tarkon wasu ’yan bindiga a garin Radda inda daga suka tasa keyarsa zuwa wani jeji a Jihar Zamfara.

Wani dan uwansa, Mustapha Radda, ya inganta rahoton wanda a cewarsa, an sako shi ne a ranar Talata da daddare kuma a halin yanzu ana bincikar lafiyarsa a asibiti.

“Yau da safe na samu labarin an sako shi sai dai ba ni da wani cikakken bayani dangane da yadda ta kasance yayin kubutarsa,” inji Mustapha.

A daren ranar Juma’ar makon jiya ce wasu ’yan bindiga suka kai simame garin Radda inda suka sace Mai Garin wanda bayan ya shafe kwanaki hudu ya kubuta.

Aminiya ta ruwaito cewa, Mai Garin ya samu damar ci gaba da rike wayarsa ta salula yayin da yake hannun masu garkuwar, inda ya kirayi iyalansa ya kuma tabbatar musu da cewa yana cikin koshin lafiya a wani jeji cikin Jihar Zamfara da yake tsare.