✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai doya

Wata rana ce wani alkali yana warware wata shari’a, kansa ya yi zafi sai wani bakauyen mai tallar doya ya zo wucewa, ya leko cikin…

Wata rana ce wani alkali yana warware wata shari’a, kansa ya yi zafi sai wani bakauyen mai tallar doya ya zo wucewa, ya leko cikin kotun ya ce: “A sai doya!” Alkali ya ce a zo masa da mai doya. Ya ce masa: “Ka san ko surutu ba a yi a kotu amma ka zo kana tallar doya? Saboda haka za a daure ka a gidan yari tsawon wata uku.” Mai doya ya ce: “Daga cewa a sai doya?” Sai alkali ya ce: “Wata shida.” Mai doya ya sake cewa: “Doya fa na ce a saya.” Sai alkali ya ce: “Wata tara.” Ran mai doya ya baci, sai ya ce: “To a sai doyoyi.”

Daga Usman dangundumar Jama’are, 08163055770