Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, wadda ke ikrarin ita ce “giwar Ifrikiyya,” ta kasura ta yi zumbutu, amma yawancin Haurobiyawa da ke adawa da wannan ‘jar miya,’ da masu udunloko da Baba-ojo da Banga-Banga Tukururu ke kwasar gararuma na ta kwakwazon ta dargaje. Don haka yau makarantarmu ta Dodorido da ke farfajiyar Amintattar jaridar kasar Haurobiya za ta yi wa masu gurgun karatun wasikun jakin dawa da na gida ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege.
’Yan makaranta ina fatan kun fasko cewa mai dan boto da sanda jirge ta yi zumbutu, don tana son aron faden tsohon kolo, ta yi fanfalaki irin na butu-butu. Giwar Ifrikiyya, wadda a halin yanzu ta kusa zama “akuyar Haurobiya,” zumbutunta ya kerata. Domin jiga-jiganta karkashibn jagorancin Baba Manga, wanda a makaranta muke yi wa lakabi da Banga-Banga Tukururu suna ta kara kwazo wajen sauya kamannu daga “giwar Ifrikiyya zuwa kazar Haurubja,” tunda sun ki yin amanna da bukatun wadanda suka ware a cikin zumbutu. Farfesun Jirin Gana ya kasa hawa motar Gano. Wannan takaddama da ake tafkawa tsakanin mai dan boto da zumbuunta yana ta daukar sabon salo, rikicin safe daban, na almuru daban.
Su kuwa jaruman majigin zumbutun mai dan boto da sanda jirge, karkashin jagorancin tsohon mataimakin Baba Ojo da Gwamna Mai kwarankwatsin siya na birnin Dabo da Baban-gada-gada mai burga da baragada na Jihar Ni-na-naja da Baba mai mongoro, wai sun ja daga kan lallai sai an sauke Baba-manga daga mukaminsa na shagaba, wai don kada ya shagabansu; kuma wajibi ne Shugaba Jatau mai sa-in-sa ya daina gudun-loko da al’ummar kasar nan. Watakila dai manufar jaruman zumbutun dan boto, ita ce a ba su jan ragamar kasar nan.
A matsayina na babban direban alli, a wannan farfajiya ba hurumina ba ne in ce ku goyi bayan zumbutu ko akuyar Ifrikiya, wadda ta dauko hanyar wargajewa. Babban al’amari da ya shafemu, shi ne ya za mu zakulo zakakuran mutane, masu manufa tagari, da za ta yi mana maganin Bobo da kwambon bokoko ta shafe shekaru sili da tsayuwa bisa kafa daya tana yi wa gama-garin al’umma; wane ne zai yi mana maganin miyagun dokokin dukan al’umma a birni da karkara; Yaya za a hana rabe-raben kawunan al’umma a tsakanin addini-adini da kabila-kabila?
A nan na fasko cewa idan jam’iyya mai kararrawa ta fasko miyagun ayyukan da Mai danboto da sanda jirge ta tsuwurwurta a kasar Haurobiya, musamman kwashi-kwaraf, wajen neman gararrumar jar-miya da raba juhala buhu-buhu ga al’umma; ga tsarin mayar da ma’aikata mahaukata, da sauran ayyukan tafka ta’asa a kwanon tasa, sai a kiyayi sa-in-sa. Mun zauna mu sasanta, ta yadda kowa zai hadiyi mai kararrawa, wadda za ta rika kadawa da zarar an zo zaluntar talakawa.
Haurobiyawa, ku sani wannan gwamnati ta raba al’ummar kasar gida karamin lauje, inda wasu suka zama ’yan bora, wasu kuwa ’ya’yan mowa. Yau abin da zai sanya ka samu kwadago ko kwantiragi a wurin gwamnatin Haurobiya shi ne, ka kasance dan yankin Hauren-Danja, ko kuma wani jigo a cikin jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Shugaban kasar Haurobiya, ya kasa fasko cewa shi ja-gaba ne na gama-garin al’umma, ba na wani yanki ba.
Jam’iyyun adawa, ya kamata ku rage laluben dawa, don kada a sake kwatawa, wato ‘adawa in ba dawa, sai a shiga dawa.’ Duk wanda ya sake kwatawa a wannan karon, maimakon dawa, sai dai a bashi daddawa. Lallai ku sani wannan danbarwa duk harigido ne na dauke hankalin al’umma daga ta’asar da suka tafka a tsawon shekarun mulkinsu na damo-da-kura-da-diyya, inda suka yi ta dama-dama da kurda-kurdar siyasa da wasan Samson-siya-siya da kwakwalen mutane. Mu dai mun gaji da gafara sa, ban ga kaho ba. Abin da giwa ta kasa gyarawa, da wuya zumbutunta ya gyara, sai dai kawai su yi ’yan gyare-gyare irin nag yare da kurege; gyare na damun al’umma da tsuwwa, alhalin ya jefa su cikin tsomomuwa, shi kuwa kurege yana ta sace musu gyada. Don haka da Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge da sabon zumbutunta, fafutika suke yi ta sabi zarce, wato dai ‘kusu ya sayi kayan kusu.’ Muna rokon Mai-duka ya raba da cinikin tasar uwargidan falken dare. Muna neman katangar karfe tsakaninmu da masu walagigi da gigita al’umma. Mai-duka ya kare mu daga juyin masar uwargidan mai sana’ar na-duke.
Haurobiyawa lokaci ya yi da za ku samar wa kanku mafita, idan kuna sha’awar mai danboto ta ci gaba da jirga al’umma, ai ba sai kun tsaya a layukan kada kuri’un zabi-sonka ba; ku bari kawai su kattaba wa jam’iyyarsu kuri’un lashe zabuka. Idan kuna sha’awar talalar talauci, ku yi dan wuya zololo kamar rakumi-rakumi zololo, har ku kasa cin naman talo-talo, sai ku bar jiga-jigan mai dan boto su ci gaba da wadaka. Kada wanda ya kara daga musu kara. Kun ga da sun gama artabu a tsakaninsu, sai kuma su juyo kanku. In ba ka yi, ba ni wuri!
Haurobiyawa, a motsa! A motsa! A motsa! Lallai ina gaya muku! To kun ji ehe!
Sakonnin makaranta:
Gangamin dalibai
Assalamu alaikum daliban makarantar dodorido a ko ina su ke muna mika godiya da bada hakuri don baza na mujiya tsawon lokaci a wannan makaranta mai albarka don kwankwadar albarkar makaranta. Muna shelanta wa dalibai gangami, kamar yadda aka saba yi a cikin kwaryar jahar Tumbin giwa. a kwanar Gaba-da-gari makaranta Sheikh Musa Ali Islmic Foundation Ranar da aka haifi danladi 08/09/2013, da misalin karfe 3:30 na yamma. Mai-duka Ya ba da ikon zuwa amin. Daga Jami’in hulda da jama’a na kasa da jaha Aliyu Mukhtar Sa’idu 08034332200.
Jaje
Assalamu alaikum Malam Dodo uban dodanni,da daukacin ‘yan wannan makaranta ta mai albarka.a madadin daliban malam na Jihar Yawon-Bebe muna ja janta wa Dodo uban dodonni, bisa wasu baki da ya yi a makonnin da suka arce. Mai duka ya kiyaye gaba, kuma ya yi mana katangar karfe da su, kuma ya mayar masa da alkairi. Daga Saka-ka- tare na Jihar Yawon-Bebe, Abubakar Charismatic, Sardaunan Matasa 07037865413.
dauki dai
Assalamu alaikum ‘yan uwana daliban makarantar Mallam Dodo ko in ce Babba Direban allin Amintattar jarida Aminiya. Da fatan anyi sallah cikin hakuri da juriyar halin da ‘yan usege tsakanin malam-mai-dauriya da samun kansu cikin wata annoba ta iska da ruwa da yawan jama’a suka rasa muhallinsu, sun sulmiye, har da kadarorin su. Muna kira da Babban Gwamna mai sunnan Sulalla na Jihar Jijjiga-ciwa da ya kawo dauki, tun kafin jama’a su jigata. Daga Shagaban dalibai na Jahar Jijjiga-ciyawa Dahiru 07039267379 /08024261439.