✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai dabara

Wani Babarbare ne ya kai matarsa haihuwa asibiti, ta yi yunkurin haihuwa ta kasa sai likita ya ce wa mijin ya kawo kudi za a…

Wani Babarbare ne ya kai matarsa haihuwa asibiti, ta yi yunkurin haihuwa ta kasa sai likita ya ce wa mijin ya kawo kudi za a yi mata tiyata a cire dan. Babarbare ba shi da kudi, ya rasa yadda zai samu kudi. Sai ya ce wa likita yana so ya yi magana da matarsa. Da ya shiga sai ya yi mata magana a kunne. fitowarsa wa je ke nan sai ta yunkura ta haihu. Likita yatambaye shi cewa: “Me ka fada wa matarka ne?” Sai ya ce: “Na fada mata cewa, kina haihuwa zan kara aure.”

Daga Sani Babawuro Jama’are, 08093435003