✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahukuntan United sun fara gajiya da dabi’un Mourinho

Mahukunta kulob din Manchester United na Ingila sun faragajiya da irin halayen da kocinsu Jose Mourinho yake nuna wa a lokacin da wasa ke gudana…

Mahukunta kulob din Manchester United na Ingila sun faragajiya da irin halayen da kocinsu Jose Mourinho yake nuna wa a lokacin da wasa ke gudana inda alkalan wasa ke yawan ba shi jan kati kuma ake yawan cin tararsa.
Jose Mourinho wanda ya samu katin kora daga fili sau biyu a tsakanin wata daya, an sake ba shi katin kora a karo na uku ne a ranar Lahadin da ta wuce a wasan da kulob din ya yi da na West Ham United a gasar firimiyar Ingila.  An tashi wasan ne da ci 1-1.
Shi dai Mourinho ya harzuka ne a lokacin da alkalin wasa ya ba Paul Pogba katin gargadi (Yellow Card) saboda karyar faduwa da ya yi da gangan ba tare da an taba shi ba (dibing) .  Hakan ce ta sa Mourinho ya yi kwallo da robar ruwa don nuna bacin ransa shi kuma alkalin wasan bai yi wata-wata ba ya daga masa jan kati.
Yanzu an dage Mourinho daga tsayuwa a kan layi a wasan da United za ta yi a gasar firimiya na gaba baya ga tarar kudin da Hukumar kwallon kafa ta Ingila  (FA) za ta kakaba masa.
Wadannan dabi’u da kocin yake yawan nunawa ne suka fara harzuka mahukunta kulob din na Manchester inda suka fara tunanin daukar mataki a kan kocin.
Mahukunta United sun nuna damuwa a kan yadda har yanzu kocin ya kasa daga martabar kulob din tun bayan da ya gaji tsohon koci Loius ban Gaal.  Kawo yanzu United ta hada maki 20 ne kacal a wasanni 13 da ta yi a gasar ta firimiya kuma wannan shi ne sakamako mafi muni da kulob din ya samu tun bayan wanda ya taba samu a kakar wasa ta 1989 zuwa 1990 watau kimanin shekaru 27 da suka wuce.