✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Mahrez kuma ya lashe Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana

An zabi dan kwallon Aljeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Leicester City na Ingila kwallo, Riyad Maharez a matsayin Gwarzon dan kwallon…

An zabi dan kwallon Aljeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Leicester City na Ingila kwallo, Riyad Maharez a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana.

A ranar Litinin da ta gabata ne Gidan Rediyon BBC ya bayar da sanarwar Mahrez ne ya lashe gasar bayan ya doke abokan takararsa Pierre Emerick Aubameyang, dan Gabon da ke yi wa kulob din Borussia Dortmund na Jamus kwallo da Amdre Ayew na Ghana da ke buga wa kulob din Swansea City na Ingila da Sadio Mane dan Mali da ke buga wa Liberpool kwallo da kuma Yaya Toure dan Kwaddebuwa da ke yi wa kulob din Manchester City na Ingila kwallo.
Mahrez, dan kimanin shekara 25 a tattaunawar da gidan rediyon BBC ya yi da shi jim kadan bayan ya lashe gasar ya ce “na yi matukar murna da kuma yin alfahari da na lashe wannan gasa”.
“Abin farin ciki ne ga duk dan kwallon Afirka ya lashe irin wannan gasa, don tana karfafa masa gwiwa,don haka ina godiya ga magoya bayana da suka zabe ni”.
Mahrez dai ya lashe wannan gasa ce bayan ya taimakawa kulob din Leicester City wajen lashe kofin firimiyar Ingila a karon farko da hakan ta sa ya doke abokan takararsa.
Kafar watsa labaran BBC kan shirya wannan gasa ce ga ’yan kwallon Afirka da ke wasa a sassan duniya, musamman Nahiyar Turai.
Masoya kwallon kafa a sassan duniya ne suke kada kuri’a wajen zaben Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC a duk shekara.