Marigayi Mahmud Tukur, tsohon Shugaban Jami’ar Bayero dake Kano (BUK) na farko kuma tsohon Ministan Kasuwanci daya ne daga cikin dattawan Najeriya da suka kafa tarihi da dama.
Kafin rasuwarsa yana da shekaru 82 a duniya ranar Juma’a, tara ga watan Afrilun 2021, marigayi Mahmud Tukur ya kasance masani, dan gwagwarmaya, dan siyasa kuma dattijo.
Makusantan marigayin sun ce sakamakon kusancinsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tarihin siyasar Buharin ba zai cika ba ba tare da an ambaci sunan Mahmud din ba, saboda irin rawar da ya taka a gwagwarmayar siyasarsa.
A zamanin mulkin Buharin na soja tsakanin shekarun 1983 zuwa 1985, marigayin shine ya kasance Ministan Kasuwanci a gwamnatinsa.
‘Shine ya yi sanadiyyar hada Aisha da Buhari’
Sai dai wani abu da mafi yawan mutane ba su sani ba shine Mahmud Tukur ne ya yi sanadiyyar hada auren Aisha da Buhari.
A cikin littafin tarihinta da Hajo Sani ta wallafa a kwanakin baya, Aisha Buhari ta bayyana yadda ta hadu da Shugaban Kasar har suka kai ga yin aure a shekarar 1989, ko da yake makusanta sun ce Mahmud ya taka muhimmiyar rawa wajen hada su, kasancewa kamar Aishan, shima daga jihar Adamawa ya fito.
“Abu ne da yake a zahiri cewa daga cikin makusantan Buhari, marigayi Mahmud ne ya hada shi da matarsa ta yanzu wato Aisha, ya taka muhimmiyar rawa a alakarsu,” inji wani makusancin iyalan Shugaban Kasar.
Yadda ya raba gari da Buhari
Wasu majiyoyi sun ce Mahmud Tukur daga bisani ya raba gari da Shugaba Buhari ne bayan wata rashin fahimta da ta barke tsakaninsu a kan batun sake tsayawarsa takara.
A lokacin da Buhari ya yi yunkurinsa na farko na tsayawa takara, Mahmud na daya daga cikin wadanda suka tsaya tsayin daka wurin tallata shi ga ‘yan Najeriya.
To sai dai bayan Buharin ya jarraba har sau uku amma bai yi nasara ba, sai marigayi Mahmud ya ba shi shawara da ya hakura ya bar matasa masu jinni a jika su jarraba sa’arsu.
Da farko dai an ce Buharin ya so ya karbi shawarsa lokacin da ya ce ba zai sake tsayawa ba in bai yi nasara a zaben 2011 ba.
Sai dai daga bisani, wasu mutanen sun sami nasarar sauya masa tunani inda ya amince zai sake tsayawa takara a 2015, lamarin da ya sa Mahmud din ya raba gari da shi kuma ya ci gaba da zama a kan bakarsa har bayan cin zaben.
Gwagwarmaya da nasororinsa
Dan asalin Yola a jihar Adamawa, an haifi Mahmud Tukur a shekarar 1939, kuma ya yi digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa da Huldar Kasa da Kasa a Jami’ar Wales dake Burtaniya.
Ya kammala digirinsa na biyu a Jami’ar Pittsburgh ita ma a Burtaniyan, sai kuma digirin digir-gir a fannin Gudanarwa daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Ya kasance shugaban Jami’ar Bayero dake Kano na farko lokacin da aka kafa ta.
Yadda Obasanjo ya katse wa’adin mulkinsa a BUK
A cikin ta’aziyyarsa ta rasuwar mamacin, Malam Mamman Daura, dan uwan Shugaba Buhari, ya bayyana yadda marigayin ya ki karbar tayin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo na zama shugaban Jami’ar Legas, ya kuma ajiye wanda yake kai a BUK nan take.
Mamman Daura ya ce, “Babu wani abu da yake bayyana Mahmud kamar jajircewarsa da kishin kasa. Ya rike mukamai da dama, ciki har da Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikata na Yankin Arewa, Shugaban Cibiyar Gudanarwa ta Kongo, wacce reshe ce ta Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, kafin daga bisani ya zama shugaban Jami’ar Bayero, ko da yake daga bisani an nada shi shugaban jami’ar Legas amma ya ki karba saboda ya ce ba a bi ka’ida ba.
“Daga karshe an yi wa wa’adinsa a BUK yankan kauna saboda shawarar Obasanjo kan tura shi Jami’ar Legas, yayin da Farfesa Akinkugbe kuma aka tura shi ABU. Amma Mahmud ya ki amincewa sannan ya ajiye mukamin.
“Na fara haduwa da Mahmud Tukur ne a 1958 lokacin da aka hada mu a Kano za a kaimu Ingila domin karo karatu. A lokacin Sardauna ne ya zabi mutum shida, wadanda sune zakaru a makarantunsu domin tafiya karatun. Mutanen sun hada da: Mahmud Tukur, Tiamiyu Salami, Abubakar Alhaji, Augustine Yange (wanda yanzu ake kira da Abdullahi Yange), Shehu Ibrahim da kuma ni.
“Tukur mutum ne mai hazaka sosai, ko a Ingilan ma wurin karatu ya yi zarra matuka, lamarin da ya jawo masa daukaka a gida da waje,” inji Mamman Daura.