Masu sana’ar gasa nama da ya hada da tsire, balangu, kilishi da kuma kaji, sun koka a kan yanayin da su ka samu kansu a yankin babban Birnin Tarayya Abuja, inda su ka yi zargin daura masu kudin haya mai tsanani a kebabbun wuraren shakatawa na birnin.
Har ila yau, sun koka kan kama mambobinsu da suka ce a ke yi tare da tsare su a gidajen kurkuku idan su ka kafa wurin sana’a a waje da ban a shakatawa ba. Shugaban kungiyar na yankin birnin tarayya, Alhaji Musa Sulaiman ne ya bayyana korafin a yayin wata ganawa da Wakilin Aminiya.
Alhaji Musa Sulaiman ya ce a lokacin da aka gudanar da rushe-rushe a birnin tarayya, gwamnatin yankin ta yi masu alkawarin sama masu wuraren dindindin da za su gudanar da sana’arsu ba tare da tsangwama ba, sai dai a cewarsa bayan tsohon ministan birnin Malam Nasir el-Rufa’i ya bar ofishin, alkawarin da a ka yi masu ya kasa samuwa.
Ya ce tarin kudi da masu gudanar da wuraren shakatawa a birnin wanda aka fi sani da “garden” ke amsa a hanunsu a matsayin kudin haya na shekara wanda ya ce ya kama daga Naira 500,000 zuwa miliyan daya. Haka nan inji shi mafi yawan mambobinsu wadanda ke gudanar da sana’arsu a gefen tituna na Abuja a sakamakon tsadar kama matsuguni a wuraren shakatawar, na fuskantar tsangwama daga hannun jami’an hukumar duba gari na birnin, “wanda ke kamasu tare da gurfanar da su a kotun tafi da gidanka, sannan a karshe a aikata da su kurkuku, bayan an lalata masu abubuwan sana’arsu,” inji shi.
Ya roki gwamnatin da ta kawo masu dauki wajen sama masu wuraren dindindin da za su yi sana’a ba tare da fuskantar tsangwama ba. Wakilinmu ya nemi jin ta bakin hukumar tsabtace mahallin birnin, inda wani jami’i a sashinta na kiwon lafiya ya bayyana cewa, dokarsu ta hana sayar da kayan abinci a wurare marasa tsabta. Ya ce yawanci masu sayar da naman na kafa tukubarsu ta gashi ne a gefen titi kusa da magudanun ruwa.
A nasu bangaren, sashen da ke kula da wuraren shakatawana birnin wato (Park and Recreation Department) sun bayyana cewa sana’o’i da dama da ake gudanarwa a wuraren shakatawar, sun sabawa dokar kafa wuraren. Sai dai ya ce matsalar korafin kudin haya mai tsada da kungiyar masu naman su ka yi, al’amari ne da ya shafi wadanda ke gudanar da sana’a a wajen, ya ce aikinsu shi ne bada waje da kuma tsara dokokin gudanar da shi, ba yin shish-shigi a kan yadda masu wuraren za su zauna da masu hayarsu ba.
Mahauta sun koka kan tsadar kudin haraji a Abuja
Masu sana’ar gasa nama da ya hada da tsire, balangu, kilishi da kuma kaji, sun koka a kan yanayin da su ka samu kansu a…