✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun yi wa manoma 10 kisan-gilla a Neja

Mazauna yankin sun koka kan yadda maharan ke musu kisan-gilla.

’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Wayam da Belu-Belu a Ƙaramar Hukumar Rafi da ke Jihar Neja, inda suka kashe aƙalla manoma 10, ciki har da mata, sannan suka sace wasu.

Harin ya faru ne da safiyar Talata lokacin da mutanen ƙauyen ke sallar Asuba.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa an sare kan mutum shida daga cikin waɗanda aka kashe.

Hakazalika sun ce maharan sun jikkata wasu da dama.

Bala Tukur, ɗaya daga cikin mazauna yankin, ya bayyana cewa, “Sun kashe mutum 10 ba tausayi. Kowa ya tsere. Samun damar girbe amfaninmu yanzu zai yi wuya.”

Harin ya kawo cikas ga aikin noma a yankunan, inda wasu mazauna yankin aka tilasta musu biyan kuɗin haraji kafin shiga gonakinsu don girbe amfanin gona.

’Yan bindigar sun kuma kai hari garin Zungeru inda suka sace mutane da dama, ciki har da Indiyawa biyu da ke aiki a gonar shinkafa a Borgu.

Gwamnatin Jihar Neja, ta sanar da cewa tana sane da lamarin, inda Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed ya yi ƙarin haske kan lamarin.

Ya ce, “An tura jami’an tsaro domin su magance matsalar da kuma hana ta sake faruwar hakan a gaba.”