✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai wa tsohon Gwamnan Imo harin bom an kashe ’yan sanda 4

Maharan sun kashe ’yan sandan da ke tsaron Ohakim ne a hanyarsa ta dawowa daga Orieagu da ke ankin Ehime Mbano 

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda hudu da ke tsaron tsohon Gwamna Jihar Imo, Ikedi Ohakim.

A ranar Litinin ne ’yan bindigar suka kashe ’yan sandan da ke ayarin motocin tsohon gwamnan a hanyarsa ta dawowa daga Orieagu da ke yankin Ehime Mbano.

Shaidu sun ce maharan ba su kai ga Ohakim ba, amma sun tayar da motar ’yan sandan da ke masa rakiya da bom, sannan suka banka mata wuta.

Hakan ne ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan sanda hudu da ke masa rakiya kuma  yana tare da ’ya’yansa biyu a lokacin da aka kai masa harin.

Shaidu sun ce ba don jarumtar direben Ohakim, wanda shi ne Gwamnan Jihar Imo daga shekara 2007 zuwa 2011 ba, da maharan sun kai gare shi.

Majiyar ta ce, daga baya tsohon gwamnan ya kira waya an turo masa karin jami’an tsaro, bayan maharan sun tsere

Kawo yanzu dai babu tabbacin ko gidan Ohakim da ke Okohia a Isiala ko kuma Owerri, hedikwatar jihar, za shi lokacin da abin ya faru.

Zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton, ba mu samu kakakin ’yan sandan Jihar Imo, CSP Mike Abatttam, ba, ballantana ya yi mana karin bayani.

Mun kira wayarsa amma bai dauka ba, haka kuma ba mu samu amsar rubutaccen sakon da muka aike masa ba, har muka kammala hada wannan rahoton.