✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe ’yan banga 4 a Kaduna

Maharan sun kashe mutanen ne a yayin da suke kan hanyar zuwa gonakinsu.

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe ’yan banga hudu da wasu manoma biyu a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 9 zuwa 10 na safe, a wani gari da ake kira Jangali.

Tsohon Kansilan yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce mutane da dama sun tsere daga yankin bayan “An kashe mutum shida yau (Talata) a Jangali lokacin da suke kan hanyar zuwa gona, kuma hudu daga cikinsu ’yan banga ne, biyu kuma manoma.

“Wannan na zuwa ne bayan wani hari da ’yan bindiga suka kawo tare da sace mutane masu yawa lokacin da suke aiki a gonakinsu a ranar Lahadi da Litinin,” a cewarsa.

A cewarsa, jama’ar yankin na cikin wani mawuyacin hali sakamakon hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa yankin a kullum.

Farmakin na zuwa ne sa’a 72 bayan wani hari da mahara suka kai yankin a ranakun Lahadi inda suka sace mutane da dama.

Ya roki gwamnati da ta kai musu dauki tare da samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Birnin Gwari baki daya.

Wakilinmu bai samu jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba domin karin bayhani.