Akalla mutum 50 ne aka rawaito sun rasa rayukansu a sakamakon wani hari da ’yan bindiga suka kai a kauyen Kachiwe da ke gundumar Sarkin Pawa ta Karamar Hukumar Munya a Jihar Neja.
Wata majiya daga yankin ta shaida mana cewa maharan sun shiga yankin da misalin karfe 10:00 na dare ranar Talata, inda suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.
- Gwamnonin Arewa sun yi daidai kan karba-karba a 2023 —Matasa
- Najeriya A Yau: Tsarabar Zamfara: ‘Da Shiga Jihar Za Ka Ga Damuwa’
“Sun zo lokacin da ake tsaka da maka ruwan sama. Kowa yana gida a lokacin, suka mamaye kauyen da harbi ta ko’ina. Sun harbe wadanda suka yi kokarin tserewa nan take. Akalla mutum 50 sun mutu yayin da dama suka ji rauni,” a cewarta.
Kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Amma Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar mana cewa, “Gaskiya ne an kai hari. An kone wasu gidaje sannan da dama sun ji rauni, yanzu haka suna asibiti suna samun kulawa.”
Sai dai ya jadadda kokarin da gwamnatin jihar ta ke yi kan sha’anin tdaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.