Akalla mutum uku ne aka tabbatar sun mutu a farmakin da wasu mahara suka kai kauyukan Amtawalam da Pobaure na Karamar Hukumar Billiri a Jihar Gombe.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Gyaran Tarbiya na Jihar Gombe, Adamu Kupto Dishi, ya ce wasu bata-gari da ba a san ko su waye ba ne suka kai harin da talatainin daren Juma’a.
Shi ma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Oqua Efiom Etim, ya ce ya ziyarci yankin da abin ya faru tare da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya kuma ya tabbatar da mutuwar mutum uku da asarar dukiya mai yawa.
Adamu Kupto, wanda ya sanar da hakan bayan zaman majalisar zartarwar jihar, ay ce, Allah ne ya takaita, da abun yafi haka.
Ya ce da aka kira shi nan take ya kira ’yan sanda da sojoji da maharba suka shiga yankin don shawo kan matsalar.
Kwamishinan ya ce da gari ya waye Gwamna ya tura su kauyukan sun gane wa idonsu irin barnar da aka yi, sannan aka umurci Hukumar Ba Da Agajin Gaugawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta ba wa wadanda abin da ya shafa tallafi don rage musu radadin asarar da suka yi.
A cewarsa, an shawo kan lamarin amma jami’an tsaro suna ci gaba da bincike dan gano wadanda suka yi aika-aikar.