✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun fasa gidan yari sun saki daruruwan fursunoni a Oyo

Daruruwan fursunoni sun tsere bayan an kai hari da abubuwan fashewa.

Daruruwan fursunoni sun tsere bayan mahara sun fasa babban gidan yarin da ke Jihar Oyo da tsakar dare.

Mazauna garin Oyo sun shaida mana cewa maharan sun yi amfani da ne abun fashewa ne wajen balla babbar kofar shiga gidan yarin da misalin karfe 10 na dare ranar Juma’a.

Shaidu sun ce ganin hakan ne ya sa jami’an tsaron da ke cibiyar neman mafaka domin tsira da rayuwarsu.

Aminiya ta gano cewa maharan sun saki daukacin fursunonin da suke gidan yarin.

Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Yari na Jihar Oyo, Olanrewaju Anjorin, ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar harin inda ya ce, “Tabbas. Hakika hakan ya faru.

“A halin yanzu Kwanturolan Hukumar Kula da Gidajen Yari da manyan jami’an hukumar na tantance abin da ya faru. Amma tabbas da gaske abin da ya faru ke nan,” kamar yadda ya shaida mana ta waya.

Matsalar tsaro dai ta dabaibaye sassan Najeriya, lamarin da Gwamnatin Tarayya ta ke ta kokarin shawon kansa.

Kawo yanzu dai babu tabbacin wanda ya kai harin, wanda ke zuwa sa’o’i kadan bayan gwamnatin ta sanar cewa akwai alaka tsakanin kungiyar Boko Haram da mai karajin neman kafa kasar Yarabawa zalla ta Oduduwa, wato Sunday Igboho, wanda sunansa na asali Sunday Adeyemo.