✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahajjatan Najeriya dubu 40,821 sun dawo gida- NAHCON

Hukumar Jindadin Alhazan Najeriya ta Kasa (NAHCON) ta ce ta dawo da alhazan Najeriya  dubu 40,821 gida Najeriya daga kasar Saudiyya bayan kammala aikin hajjin bana…

Hukumar Jindadin Alhazan Najeriya ta Kasa (NAHCON) ta ce ta dawo da alhazan Najeriya  dubu 40,821 gida Najeriya daga kasar Saudiyya bayan kammala aikin hajjin bana na shekarar 2019  cikin nasara.

Cibiyar hukumar NAHCON da ke birnin Makkah ce ta sanarwa Kamfanin Dillancin Labarai NAN hakan yau Litinin. Mahajjatan da suka dawo gida na karshe a yazu su ne alhazan jihar Filato 555 tare da jami’an NAHCON a jirgin saman Max Air flight NGL 2110.