✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Sheikh Kabiru Gombe ta rasu

Za a yi jana'izarta a Masallacin JIBWIS da ke Bolari a gobe Juma'a da misalin karfe 1:30 na rana.

Hajiya Fatima Abdullahi Haruna, Mahaifiyar Babban Malamin nan Izala, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ta rasu a yau Alhamis, a jihar Gombe.

Ministan Sadarwa kuma daya daga cikin Manyan Malaman Izala, Sheikh Dokta Isa Ali Ibrahim Pantami, ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Hajiya Fatima mai shekaru 75 ta rasu da misalin karfe 5:30 na Yammacin Alhamis kuma za a yi jana’izarta a masallacin Kungiyar Jama’atu Izalil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) da ke Bolari a gobe Juma’a da misalin karfe 1:30 na rana.

Sheikh Pantami ya yi addu’ar Allah ya yafe mata kurakuranta Ya kuma azurta ta da Rahama.

Ya wallafa cewa, “Allah Ya kyautata namu bayan na su Ya kuma jikan iyayenmu.”