Mahaifin almajirin nan da aka yi wa tabbai kaca-kaca da bulala a jiki ya ce bai ma san cewa dansa yana Kano ba sai bayan da ya kalli bidiyonsa a Facebook.
Almajirin, wanda ma’aikacin gidan rediyon Freedom, Nasiru Salisu Zango ya sanya bidiyonsa a daren ranar Lahadi ya bayyana cewa malaminsa ne ya ke zane shi da bulala duk lokacin da ya je bara bai samo wa malamin abinci ba.
- Dokta Mariya Bunkure: Fafutuka wajen sama wa mata ilimi tun daga tushe
- Babu gwamnatin da ta taba rayuwar ’yan Najeriya irin ta Buhari – Abdullahi Adamu
A cikin bidiyon, an nuna yadda aka yi wa yaron mai suna Muhammadu da bai wuce shekara takwas da haihuwa ba dan asalin Jihar Bauchi kaca-kaca da duka a jikinsa.
“Malamin mu ne ya ji min wannan ciwon saboda bana kawo abinci, in ban samo abinci ba na ce a kai ni gida,” cewar Almajirin.