Dubban matasa ne suka yi bore a Karamar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe sannan suka kona tsintsiya, alamar jam’iyyar APC mai mulki.
Matasan dai na zanga-zangar ne saboda neman tsohon dan takarar Gwamnan Jihar a zaben 2019 karkashin jam’iyyar PDP, Dokta Jamilu Isyaku Gwamna ya bar APC.
- Tawagar Shugaban Kasa ta je ta’aziyyar Dokta Ahmad Bamba
- Kwallon kafa: Ranar Lahadi gwanayen Afirka za su fara artabu a Kamaru
Matasan, wadanda ’ya’yan jam’iyyar ta APC ne, sun yi kira ga tsohon dan takarar da ya fice daga jam’iyyar ya koma wata, za su mara masa baya.
A zantawarsa da manema labarai a Gombe, daya daga cikin magoya bayan dan takarar, Isah Kaltungo, wanda ya hada magoya baya sama da 200 a Karamar Hukumar Kaltungo wajen koma tsintsiyoyin.
Isah Kaltungo, ya zargi shugabanin jam’iyyar ta APC a Jihar da hada kai wajen kokarin sake amincewa su sake tsayar da Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya a matsayin gwamna karo na biyu a Jihar.
Ya kuma zargi wasu Kananan Hukumomi na Jihar, cikinsu har da Kaltungo, inda gwamna ya kai musu ziyara har shugabanin jam’iyyar suka fito fili suka ce sun ayyana shi a matsayin dan takarar su a zaben 2023.
Ya ce, “Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun bayyana kudurin su na tabbatar da shi ne dan takarar su a wasu taruka daban-daban da suka gudanar a garuruwan Kaltungo da Deba da Kuma Gombe.
“Wanda hakan ke nuni da cewa basa bukatar ayi zaben fid da gwani, hakan ba zai bari ayi adalci ga sauran ’yan takara ba, domin sun riga sun ayyana shi a matsayin dan takararsu.”
A cewarsa hakan ne yasa suka shawarci Jamilu Gwamna da ya fice daga jam’iyyar ya shiga wata daban, za su bi shi kuma suna da tabbacin zai iya cin zabe domin yana da farin jini a idon masu zabe.
Kaltungo, ya kuma nesanta kansa daga cikin shugabanin jam’iyyar APC da suke ci wa Sanata Danjuma Goje mutunci wanda ya ce shi ne ya jagoranci jam’iyyar har ya kamawa Inuwa Yahaya ya ci zabe a 2019.
Sai dai da yake mayar da martani ga Shugaban jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Kaltungo, Kwamred Ayuba Hassan, ya ce bai da masaniyar wani mamban jam’iyyarsa da ya fita daga jam’iyyar har ya kona tsintsinya a yankin.
Sai dai Ayuba, ya ce jam’iyyar APC a yankinsu na kokarin yi wa mambobinta adalci har da wadanda suke kokarin fitowa takara na mukamai daban daban.
Ya ce wadanda suke wannan zargin suna jin tsoron takararsu ne kuma yanzu ya yi wuri ayi hukunci.