✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan Arsenal sun bukaci a dawo da Kanu

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sun bukaci a dawo da tsohon dan wasansu wanda ya yi ritaya daga buga wa kungiyar kwallon kafa…

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sun bukaci a dawo da tsohon dan wasansu wanda ya yi ritaya daga buga wa kungiyar kwallon kafa Nwanko Kanu.
Tohon dan kwallon Najeriya, Kanu ya zura kwallaye uku ne a wani wasa da aka buga tsakanin tsofaffin ’yan kwallon Arsenal da kuma tsofaffin ’yan kwallon kulob din AC Milan na Italiya inda kungiyar Arsenal ta lashe wasan da ci 4 da 1.
Bayan wasan ne wadansu daga cikin magoya bayan kungiyar suka bukaci lallai kungiyar ta dawo da Kanu Nwanko domin ya ci gaba da buga wa kungiyar wasa.  A cewarsu har yanzu akwai sauransa hasali ma  ya fi  da  yawa daga cikin ’yan wasan da suke buga wa kungiyar wasa a yanzu.
Daga cikin wadanda suka nuna bukatar a dawo da Kanu sun hada da wani mai suna George inda ya yi rubutu a shafinsa na Twitter  yana cewa: “Kanu ya tafi amma bayan shekara 14 ya dawo ya zura kwallaye uku sama da Giroud.”  Giroud dai shi ne dan wasan gaba a kulob din Arsenal a halin yanzu.
 Shi ma wani mai suna Anie dtian ya rubuta a shafinsa cewa “Duk da cewa Kanu ya yi ritaya, amma ya nuna ya fi Giroud hikima da kwazo, don haka ya kamata kocin Arsenal, Arsene Wenger ya dawo da shi.”