Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta raba wa magidanta kimanin 3,663 kayan jinkai domin rage radadin ambaliyar ruwan da ta ritsa da su a kananan hukumomi 13 a Jihar Zamfara.
Yayin bikin rabon kayan da ya gudana a babban birnin jihar na Gusau, babban daraktan hukumar, AVM Muhammad Alhaji Muhammad (Mai ritaya), ya ce Gwamnatin Tarayya ta raba kayayyakin ne ga mutanen da ibtila’in ambaliyar ya ritsa da su a jihar.
- Babu ko mutum daya da ya kamu da COVID-19 cikin masu Umara miliyan 5 – Saudiyya
- Ba ni da shirin ficewa daga PDP – Gwamnan Abiya
- An cafke basarake a cikin ’yan bindiga a Neja
Daga cikin kayan da aka raba sun hada da kayan abinci da tufafi da kayan gini.
Shugaban na NEMA ya ce hukumar ta su zata ci gaba da wayar da kan al’umma kan su dakatar da gine-gine a hanyoyin wucewar ruwa don kaucewa faruwar ambaliyar a nan gaba.
“Hukumar kan rarraba kayayyakin jin kai ga mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su don rage musu radadin asarar da suka tafka,” In ji shi.
Shi kuwa Jami’in Gudanarwar hukumar, Usman AbdulAziz kira ya yi ga mutanen da suka amfana da kayayyakin da su gujewa duk wata hanya da za ta saka su rasa dukiyoyinsu sakamakon ambaliyar ruwa a nan gaba.
Kayan da aka raba sun hada da buhunan siminti guda 3,250 da bandiran kwanukan rufi guda 3,250 da silin rufin daki guda 3,250 da kuma buhunan kusa guda 1,500.
Sauran kayan sun hada da buhunan shinkafa guda 3,663, da wake buhu 1,148 da gero da man girki da gishiri da katan-katan na tumaturin gwangwani da magi da kayan sakawa da tabarmi da gidan maganin sauro da bargon rufa da tabarmi.