Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta samu nasarar damke wani magidanci da ake zargi da kashe wani jariri.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya tabbatar da kama mutumin a cikin wata sanarwa da ya fitar.
- Gobarar kwala-kwale ta hallaka ‘yan ci rani a tsakiyar Teku
- Yadda ilimin mata ke samun koma-baya a Jihar Sakkwato
Wanda ake zargi ya kashe jaririn ne a yayin da aka kai wa mahaifiyar jaririn hari a ranar 29 ga watan Satumbar 2022.
“Wanda ake zargi da kisan Barnabas Abduneza mai shekara 40, mazaunin kauyen Kpasham da ke Karamar Hukumar Demsa, ya shiga hannu ne a sakamakon samun kwakkwaran bayanai,” a cewar kakakin.
Sanarwar ta kuma ce, mahaifiyar jaririn ta samu munanan raunuka, yayin da jaririn da ta ke dauke da shi ya mutu.
Rundunar ta kuma samu wanda ake zargi dauke da miyagun makamai ciki har da wuka, da kwari da baka a lokacin da kama shi.