✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidanci ya zargi ’yan sanda da kashe dansa

Wani magidanci mai suna Malam Mukhtari Musa ya zargi ’yan sanda da kashe dansa a Maiduguri fadar Jihar Borno. Mahaifin yaron ya zargi ’yan sandan…

Wani magidanci mai suna Malam Mukhtari Musa ya zargi ’yan sanda da kashe dansa a Maiduguri fadar Jihar Borno.

Mahaifin yaron ya zargi ’yan sandan kwantar da tarzoma da lakada wa dansa duka har ya kai ga rasa ransa. “A ranar Juma’ar da ta gabata dana mai suna Hassan Mukhtari, wanda bai wuce shekara 22 ba, a Unguwar Goni Kachallari, Layin Yusufu Maibulo, ya zo gida ya tarar da kannensa Abdu Muhammed da kuma Is’haku suna dukan wata akuya, sai ya ce su bari kuma su saki akuyar.  Ashe bai san cewa suna dukan akuyar bisa umarnin wani dan sandan MOPOL, sai wannan dan sanda Abdullahi ya fusata ya kama dukan dan nawa, har sai da ya kai ba ya iya komai, sannan sai ya dauke shi ya kai shi ofishin ’yan sanda na Unguwar Gwange, inda suka kai shi suka kulle shi tare da yarsa mai suna Fatima,” inj shi.

Ya ce “Da tsakar dare kuma sai suka shiga dukan Hassan suka yi masa jina-jina inda daga baya ya rasu. Washegari na kawo musu abinci a ofishin ’yan sandan sai suka ce da ni in zo in dauki gawar dana wai ya rasu, to sai na yi mamakin faruwar al’amarin. Yarsa Fatima ta ba ni labarin duk irin abubuwan da suka faru da su da tsakar dare na irin yadda suka lakada masa dukan kawo wuka, har ya kasance ba ya da wani karsashi kafin wayewar gari ya ce ga garin ku nan. Don haka nake rokon hukumomin da abin ya shafa da su yi wa Allah su bi mini hakkina.’’

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Borno, Malam Mohammed Ndatsu Aliyu ya ce ya samu rahoton faruwar lamarin kuma ya bayar da umarnin a gudanar da bincike a kai don daukar matakin da ya kamata.