✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maganin biri…

Wani Bakatsine ne da dare sai matarsa ta ce masa: “Maigida, anya kuwa ka rufe gida?” Sai ya ce bari ya je ya duba. Lokacin…

Wani Bakatsine ne da dare sai matarsa ta ce masa: “Maigida, anya kuwa ka rufe gida?” Sai ya ce bari ya je ya duba. Lokacin da ya fita tsakar gida sai ya ga barayi sun shigo, suna shirin yi musu sata. Ganin haka sai ya boye, ya kira ’yan sanda, ya gaya musu cewa: “Don Allah ku zo gidana, ga barayi nan suna neman yi mana fashi.” Sai wani jami’in ’yan sanda ya amsa masa da cewa: “Kash! Ka yi hakuri, motar faturun yanzu ta fita da mutanenmu, amma ina ba ka shawara da ka yi sauri ka rufe kofar gidanka, nan gaba kadan, idan sun dawo za ka ga sun zo.” Bakatsinen nan, bayan sakan 30 sai ya sake kiran ’yan sandan a karo na biyu, ya ce: “Ni ne yanzu na ce ’yan fashi na gidana, to kar ku damu, domin duk na harbe su duka, ga gawarwakinsu nan kwance cikin jini.” Bai tsaya jin amsa ba sai ya kashe wayar. Cikin minti biyar sai ga motocin ’yan sanda har biyu, cike da jami’ai dauke da bindigogi. Nan take suka kama barayin. Shugaban ’yan sandan ya ce: “Amma a waya cewa ka yi duk ka harbe su!” Shi kuwa sai ya ce musu: “Ni kuma da na kira ku da farko, sai na ji kamar kun ce jami’anku sun fita faturun, babu kowa!”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08098157899