✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta sanya farashin Naira Biliyan 317 a kan Ronaldo

Shugaban kulob din Real Madrid na Sifen Florentino Perez ya ce duk mai bukatar ya sayi shahrarren dan kwallonsa Cristiano Ronaldo sai ya ajiye  zunzurutun…

Shugaban kulob din Real Madrid na Sifen Florentino Perez ya ce duk mai bukatar ya sayi shahrarren dan kwallonsa Cristiano Ronaldo sai ya ajiye  zunzurutun Fam miliyan 880 kwatankwacin Naira Biliyan 317.

Shugaban ya ce tun bayan da Ronaldo ya koma gida don yin hutu jim kadan bayan an kammala kakar wasan da ta wuce inda ya taimaka wa Madrid lashe kofunan La-Liga da na zakarun kulob na Turai (Champions League) ba su yi ido hudu ba, kuma a yayin hutun ne aka sake zabar Perez a matsayin shugaban kulob din Madrid a karo na biyar a jere.

Ya ce a kwanakin baya ne ya yi mamakin yadda wasu kafofin watsa labarai suka rika yada labarin kanzen kurege cewa Manchester United tana yunkurin dauke Ronaldo, to a gaskiyar magana ita ce babu wani kulob da ya tuntubi Madrid a game da saye Ronaldo.  Shugaban ya kara da cewa don haka ne ya yanke shawarar sanya farashin Naira Biliyan 317 a kan duk mai bukatar dan kwallon a halin yanzu.

“Duk kulob din da ke bukatar saye Ronaldo sai ya ajiye zunzurutun Fam Miliyan 880”, in ji shugaban.

Kawo yanzu dai kulob din Manchester United na Ingila bai furta wani kalami game da sayen Ronaldo ba, hasalima ya karkata akalarsa ne wajen cefano wasu zaratan ’yan kwallo irin su Romelu Lukaku don tun kakar wasa ta bana.