Rahotannin da ke fitowa sun nuna kulob din Real Madrid na Sifen ya fara tunanin dawo da tsohon dan kwallonsa Mesut Ozil wanda ya sayar da shi ga kulob din Arsenal na Ingila a shekarun baya.
Kulob din ya ce zai yi zawarcin Ozil ne bayan ya sayar da dan kwallon tsakiyarsa James Rodriguez kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta Don Balon reports ta kalato.
Shi dai Mesut Ozil ya taba yi wa kulob din Real Madrid wasa ne a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013 inda ya koma kulob din Arsenal a shekarar 2013 bayan Madrid ta sayar da shi.
dan asalin Jamus Ozil, yanzu haka tauraruwarsa na haskakawa a kulob din Arsenal bayan ya taimaka wa Arsenal wajen zura kwallaye 12 a raga a duk wasannin da ya yi a kakar wasa ta bana al’amarin da ya sa ya shiga kundin tarihin kulob din.
Rahoton ya ce kulob din Madrid ya tabbatar yanzu Ozil ya samu gogewar da ya kamata a ce yana buga wa kulob din Madrid ne fiye da yadda ya yi mata kwallo a baya.
Madrid ta fara zawarcin Mesut Ozil
Rahotannin da ke fitowa sun nuna kulob din Real Madrid na Sifen ya fara tunanin dawo da tsohon dan kwallonsa Mesut Ozil wanda ya sayar…