✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid da Barcelona da Jubentus suna rububi a kan Mane

Kulob din Real Madrid da FC Barcelona dukkaninsu daga Sifen da kuma na Jubentus daga Italiya yanzu haka sun fara rububi a kan dan kwallon…

Kulob din Real Madrid da FC Barcelona dukkaninsu daga Sifen da kuma na Jubentus daga Italiya yanzu haka sun fara rububi a kan dan kwallon gaba a kulob din Liberpool na Ingila Sadio Mane.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta The Sun ta kalato, ta nuna kulob din FC Barcelona ne ya fara yunkurin dauke dan kwallon bayan ya yunkurin da ya yi na dauke Phillipe Coutinho daga Liberpool abin ya faskara.

Ita kuwa kafar watsa labarai ta The Guradian ta ce tuni kulob din Real Madrid da na Jubentus su ma suka shiga rububi a kan dan kwallon.

Sadio Mane dai tauraruwarsa tana haskakawa a kakar wasa ta bana, sai dai yanzu haka yana fuskantar dage shi daga yin wasanni hudu a gasar rukunin firimiyar Ingila saboda jan katin da ya samu a wasan da suka yi da na Manchester City bayan ya tokari golan City.