Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron, ya shaida wa takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky, cewar za su ci gaba da ba shi makamai domin kare kasarsa daga hare-haren Rasha.
Sanarwar da fadar shugaban Faransa ta fitar, ta ce kasar za ta ci gaba da bai wa Ukraine makamai, kuma za ta kara yawansu tare da kayan jinkai a cikin kwanaki masu zuwa.
Kafin wannan lokacin Faransa na jan kafa wajen bai wa Ukraine makamai, saboda rawar da Macron yake takawa na sasanci tsakanin Zelensky da Shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Ko a baya-bayan nan sai da kungiyar tsaro ta NATO, ta lashi takobin taimakon Ukraine da makamai da za ta amfani da su wajen yakar Rasha.
Tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, kasashe da dama musamman daga Yammacin Turai ke ci gaba da Allah wadai da kuma sanya wa Rashan takunkumai.
Tun ballewar yakin a watan Fabrairun 2022, dubban mutane sun rasa rayukansu, yayin da dama suka jikkata, baya ga miliyoyin mutane da suka tsere daga muhallansu.