Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya lashi takobin yakar masu ra’ayin aware na Islama yana mai barazanar kwace iko a yankunan Musulmai a kasar.
Kamfanin dillancin labaru na Reuters ta ce Faransa ta damu cewa maza Musulmai ba sa musabaha da mata, kananan yara mata na sanya nikabi makarantun Islamiyya na karuwa, wuraren ninkaya kuma na kebe lokacin mata daban da na maza a yankunan Musulmai.
“Muna bukatar yakar wariyar ra’ayin Musuluci…matsalar ita ce akidar da ke ganin dokokinta na gaba da dokokin kasa”, inji Macron a lokacin da ya ziyarci yanknin talakawa na Les Mureaux a Paris.
Ya ce zai aike wa Majalisar Dokokin kasar kudurin dokar da za ta hana karantar da yara a gida domin hana “cusa musu tsattsauran ra’ayi” a makarantu marasa rajista da suka saba wa manhajar karatun kasar.
Faransa ta sha kokarin muttsuke masu ra’ayin Islama a cikin gida marasa rikici, amma gwamnatin Macron na bayyana damuwa game da abin da ta kira tsattsauran ra’ayin Musulunci.
Tanade-tanaden sabuwar dokar sun hada da haramta wa malamai daga kasashen waje horas da limaman Faransa a kan yin wa’azi.
Za kuma ta ba wa wakilan Gwamantin Kasar a yankuna izinin kwace iko ko soke umarnin masu gari a yankunan da aka kebe gidajen wanka ko gidajen abinci ko makarantu ga maza ko mata.
Dokar za ta kafa hukumar bincike kan addinin Musulunci sannan ta ba da kwarin gwiwa wajen koyon harshen Larabci.
Shugaban kungiyar Musulmi ta Faransa, Amar Lasfar ya shaida wa Reuters cewa babu bukatar sabuwar dokar domin za a iya cimma manufar da ake bukata idan aka aiwatar da dokokin kasar na yanzu.
Sai dai ya soki Macron game da irin kalmomin da ya yi amfani da su a jawabin nasa game da yadda yake nufin yakar masu tsattsauran ra’ayin Islama a kasar.