Rataye da sandarta, sanye da gajeren wando mai launin shudi da bakar riga da kuma hular kaboyi, Misis Ekene Obaye ta kasance mace ta farko ’yar asalin kabilar Igbo da ta rungumi sana’ar kiwon shanu.
Galibi dai a Najeriya Fulani makiyaya aka fi sani da sana’ar, ba ’yan kabilar ta Igbo ba, tun ma ba ace mace ba.
- Za mu ba ’yan kabilar Igbo kariya a Kano —Sarkin Bichi
- Kirsimeti: CAN ta shawarci ’yan Najeriya su yi taka-tsan-tsan
Misis Ekene ’yar asalin garin Nguru dake karamar Hukumar Nsukka ta jihar Enugu ta sha fafutuka kafin ta shawo kan mai gidanta Patrick Obaye shima ya rungumi sana’ar ta kiwon shanun.
Misis Ekene ta shaida wa Aminiya cewa, “Muna da gonaki, kuma ba na son shanuna su yi wa kowa barna a tasa gonar. Amma kun ga wannan saniyar guda daya tana matukar sha’awar cin ganyen rogo, ba ta gajiya,” inji ta, yayin da take ci gaba da kula da shanun nata kusan su 20.
Mai digiri a fannin Sanin Kayan Tarihi daga Jami’ar Najeriya dake Nsukka (UNN), Ekene ta ce rashin samun kwakkwaran aiki da kuma hatsarin motar da ya ritsa da mijinta a watan Disamban 2019 wanda ya kusa zama ajalinsa ne suka tilasta mata shiga harkar kiwon.
Sai dai ta ce dama can iyalan mijin nata na yin sana’ar ta kiwon tun kafin ta aure shi.
Mai kimanin shekaru 38 a duniya, Ekene ta kara da cewa, “Bayan an sallame shi ya dawo gida daga asibiti, sai dai azabar ciwon ta sa ba zai iya ci gaba da kula da shanun shi kadai ba, sai ya kasance kamar kasuwancin nasa zai tasamma durkushewa kenan.
“A kan haka ne na yanke shawarar dorawa daga inda ya tsaya har ya warke.”
Yadda ta ke fadi-tashi da dabbobin
A kan yadda take fadi-tashi wajen yin sana’ar da maza aka fi sani da ita, Misis Ekene wacce aka fi kira da Nwanyi N’achi Ehi (Mace mai kiwo) ta ce, “Ba ni da wata matsala da yin hakan saboda akwai riba sosai. Ina jin dadin yi kuma ba na ma tunanin neman wani aiki saboda na sami nawa,” inji ta.
Kullum kwanan duniya dai sai ta yi tattakin kusan tafiyar da ba ta gaza kilomita 36 ba tare da dabbobin a cikin daji.
Ta ce, “Zan iya tattaki daga nan zuwa Obimo wanda ya kai kusan kilomita 36. Idan ka hada kilomita 36 sau biyu (zuwa da dawowa) zan iya yin tafiyar kilomita 72 kenan a kullum.
“Wasu lokutan ma na kan yi fiye da haka. Mu kan je har Lejja saboda garin da Obimo sun hada iyaka daya.”
‘Ranar da na fara kiwo a daji’
Misis Ekene ta tuno yadda ta fara kiwo a daji inda ta ce, “Ranar da na fara shiga daji da shanu ’yan kauyuka sun fito da addunansu suna ihun cewa ga ’yar Fulani mace mai kiwon shanu. Sun tayar da jijiyoyin wuya matuka har sai da na yi yaren Igbo na gabatar da kaina.
“Daga nan ne sai hankulansu suka kwanta suna mamakin yadda ba na tsoron shanu a matsayi na na ’yar kabilar Igbo kuma mace. Daga nan suka karfafa min gwiwa suka ce sun san miji na sosai.
A kan yadda take hada kula da dabbobin da kuma aikin gida, matar ta ce kiwon ba abinda ya hana ta a ayyukan gida saboda ita da mijinta sun raba wa kansu ayyukan yadda ya kamata.
Wata ran ta kan yi aikin gida mijin ya shiga daji, wata ran kuma ta kan shiga daji mijin ya yi aikin gida.
Ta ce, “Akwai fahimtar juna tsakani na da shi. In dai akwai ta kuma zai yi wuya a sami sabani. Hatta ‘ya’yan namu wani lokacin su kan bi ni waurin kiwon. Duk karshen mako ko ranakun hutu kuwa dukkanmu muke dunguma mu tafi, su kan debo wa shanun ruwan sha ma.”
Akan yadda take kiyaye shanun daga shiga gonakin mutane saboda gudun yi musu barna, Misis Ekene ta ce, “Akwai matsalolin da ba kudi ne ke iya warware su ba, kawai abinda ake bukata shine tattausan lafazi da mutunta masu gonakin, wannan dabarar kuma tana yi min aiki yadda ya kamata.”
Ta kuma ce babban kalubalen ta a yanzu bai wuce yadda za ta tara kudi ta gina garkar shanun ba domin su daina gararanba.
“Da ace gwamnatin jihar Enugu za ta tallafa min da kamar Naira miliyan 20 zuwa sama, zan iya gina wurin da shanun nawa za su daina yawo, muna da wadatattun filaye a nan Nguru.
“Girke dabbobin nawa wuri guda shine babban maslaha. Da ace kowanne makiyayi zai killace dabbobin sa wuri daya da an daina samun tashin-tashina tsakanin manoma da makiyaya,” inji ta.
Da aka tambaye ta ko ba ta jin tsoron shanun sai ta ce ko kun taba jin labarin a inda shanu suka kashe mutane? Ta ce shanu kamar sauran dabbobin gida ne, kuma yadda ka tarbiyyantar da su haka za su saba da kai.
“Abinda kawai yake tunzura su shine idan suka ga cincirindon mutane su kan dan firgita. Idan suka ga mutane da yawa su kan firgita su yi tunanin ko farmaki za a kai musu.”
Ta kuma ce ta kan tafi har garin Mubi a jihar Adamawa da kuma jihar Katsina domin samun sabbin irin shanun.
A cewar ta, yanzu haka tana da shanu 28 a karkashin kulawar ta, tana mai cewa ko da za a ba ta shanu 1,000 za ta iya kula da su yadda ya kamata ba tare da ko da guda daya ta bata ba.
Misis Ekene ta ce sandar kiwon ta kawai take amfani da ita wajen kula da shanun ba tare da rike kowanne irin makami ba.
A kan kalubalen da sana’ar ta ta fi fuskanta kuwa, ta ce matsalar ba ta wuce idan wasu daga cikin shanun suka kamu da rashin lafiya ba daga bisani kuma su fadi su mutu.
“Ka ga idan suka mutu, duk kudin da ka kashe wurin sayen su da kuma kiwon su sun zama asara kenan,” inji ta.