Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa a Jihar Yobe ta amince da nadin Farfesa Maimuna Waziri a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Jami’ar ta fitar a ranar Asabar dauke da sa hannun Shugaban Sashen Watsa Labaranta, Usar Ignatius.
- Sojoji sun bace bayan harin Boko Haram a Marte
- Zaben Kano: Akwai alamun nasara a duk kananan hukumomi- Ganduje
Maimuna, wacce Farfesa ce a bangaren Ilimin Sinadarai za ta maye gurbin Shugaban Jami’ar mai barin gado, Farfesa Andrew Haruna, wanda wa’adin mulkinsa zai kare a farkon watan Fabrairu mai zuwa.
Ta sami nasarar zama Shugabar Jami’ar ne bayan ta doke abokan takararta 47 a wani zazzafan zabe da ya gudana ranar Asabar, 16 ga watan Janairun 2021.
Sanarwar dai ta biyo bayan taron Majalisar Gudanarwar Jami’ar, wanda Uban Jami’ar Ibrahim Akuyam ya jagoranta.
Ibrahim ya ce mutum 48 ne suka fafata domin neman kujerar, aka fitar da sunayen mutum 25, aka zabi uku daga ciki ita kuma Majalisar ta zabi Farfesa Maimuna a matsayin sabuwar shugabar.
Daga nan sai Uban Jami’ar ya taya sabuwar shugabar murna tare da kiran ta da ta rungumi kowa hannu bibbiyu domin a ciyar da makarantar gaba.