Wata mai sun Lauren Issa sanye da kayan barci ta kwana kan tsaunin da ke kallon Masallacin Harami a Makka, sannan ta wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na intanet.
Matar ‘yar asalin kasar Siriya ta kwana a kan tsaunin ne kwanciya ta jin dadi irin ta masu yawan shakatawa, gari na wayewa, dauki hoton kanta, ta kuma sa a shafinta na Instagram.
- ‘Man da Najeriya take hakowa yanzu bai wuce ganga 1.3m ba a kullum’
- Ku ba Atiku shawara ya je gida ya huta ya hakura da takara – Tinubu
Hakan na cikin wani gajerin bidiyo ne da wasu masu kishin abubuwan da ke faruwa a kasar Saudiyya suka wallafa a shafin sada zumunta na Facebook domin ankarar da jama’a.
Hoton bidiyon matar ya nuna ta sanye da riga mai gajeren hannun da dogon wando, kanta a bude, gashinta a waje, kwance a cikin bargo wanda ta lulluba, sannan ta tashi daga shimfidar tana rangwada.
Hakan ya harzuka mutane da dama, yayin da wasu ke nuna takaici, wasu kuma na kira da a kama matar a hukunta ta da kuma wadanda suka ba ta damar hawa wannan wuri da kuma keta alfamar wurin.
Wasu kuma sun yi tir da ita, sannan suka dora alhakin hakan ga Yarima Saudiyya, Muhammad Bin Salman, da ya bayar da kofar hakan ta hanyar irin bude kofar badala da ya yi da abin da ya kira ‘sauye-sauye na zamani’.
A makwannin da suka gabata ne aka yi bikin gargajiyar Turawa na dodanni da ake kira da Halloween, aka kuma yi bikin casu a salo irin na Turawan a Riyadh, babban birnin kasar, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.