A ko da yaushe sai ka ji mata suna zargin mazaje a kan cewa wai sun kasa cika alkawari, har ka ji suna yi musu kirari da cewa namiji ba dan goyo ba ne, kuma duk matar da ta riki namiji uba to hakika za ta mutum marainiya.
Mata su kan dage da fadin dalilan cewa a lokacin da suke tsakiyar soyayya kafin aure namiji ya kan yi musu alkawarin cewa daga su babu kari.
Idan muka dubi wadannan zantuka na mata to za mu ga cewa shin mai ya jawo suke fadawa mazaje haka? Na yarda da wadannan kalmomin da mata suke jifan maza da su da zarar in an yi musu kishiya domin abubuwan marar dadi da suke faruwa ga wasu mata na rashin dadin zama da kishiya hakika shine musabbabin da ya sa suke fadar haka wasu matan su kan tsinci kansu cikin tsaka mai wuya na rashin adalci tsakanin su da kishiya.
Su kuma mazajen su kan kawo dalilai na kara yin aure domin da yawa za ka ga in an yi aure na soyayya amma da zarar Allah ya jarrabi namiji da talauci na rayuwa to sai ka ga wasu matan sun kasa hakuri sun tayar wa da mazajen hankali a karshe kuma in Allah Ya warware wa namiji watau ya fara ganin budi sai ka ga namiji zancen karin aure saboda ya huce takaicin da uwargida ta sa shi a lokacin yana tsakiyar kuncin rayuwa. Wasu kuma mazan su kan kara aure saboda kwata-kwata wata matar ba ta da kirki ba ta ganin kimar miji balle ta uwar miji ko danginsa. Wasu matan ba su iya kwalliya da tsafta sun kuma mayar da dakunan da suke kwana tamkar dakin zuba shara. Dalilin na karshe ga wasu mazan suna cewa mace daya ba ta gamsar da su don haka ba za su iya hakuri da mace daya ba.
Ko ma menene dai dole mace ta yi hakurin zama da kishiya ko da a ce ita ce ta jawo a ka yi mata kishiya ko kuma ra’ayin mai gidanta ne domin musulunci ya ba wa mazaje damar yin aure mace fiye da daya amma bisa sharadin maza su yi adalci a cikin matansu in kuma baza su iya adalci ba to yin riko da mace daya shine mafita ga kubuta ga azabar Allah.
Ina kira ga mata domin na san kishi bashi da dadi amma ya kamata ku yi koyi da matan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi da sauran matan Sahabbai.
Kishi wata dabi’a ce da Allah ya halicci mata a kanta, Nana A’isha tana
cewa : “Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yi wa Khadijah, kuma alhali ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi S.A.W yana ambatonta.”
Kishi mai tsafta, shi ne, kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta wajen kyautatawa mijinsu.
Menene ke kawo matsaloli tsakanin kishiya da kishiya, kuma ta yaya za’a warware su?
1. Jahilci : Yadda mata da yawa suka jahilci hikimomin da suka sa
Allah ya yi umarni a kara aure, kamar rage yawan zawarawa da ‘yanmata, da kuma yawaita zurriyar Annabi S.A.W.
2. Mummunan zato, yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwargida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima.
Amma idan da a ce kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba za a samu matsala ba.
2. Rashin adalci daga wajen namiji, ta yadda zai karkata zuwa ga daya daga cikin matansa, hakan sai ya sa dayar ta ce ba ta yarda ba.
Sai dai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne, babu yadda za a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya. Annabi S.A.W. Ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A’isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, su kan kirga ranakun da ya ke dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan ki ka ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki ta da fitina, sai dai abin da sharia ta hana shi ne, rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum.
3. Munafukai, masu cece kuce, idan da a ce kishiyoyi za su daina daukar gutsuri tsoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli.
Ado Musa(08069186916) mazaunin Unguwar Kaura Goje da ke Kano ne.
Mace ita take wa kanta kishiya
A ko da yaushe sai ka ji mata suna zargin mazaje a kan cewa wai sun kasa cika alkawari, har ka ji suna yi musu…