Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu bayanan da za su zo cikin sa, amin. In shaAllah yau kuma za mu kawo bayani kan siffar ma’auratan da za su dace da Ramadana. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, ya kuma amfanar da su, amin.
Ya ‘yan uwa mu sani fa wannan wata ne na amsa addu’a da karbar tuba, muna da dimbin bukatun da ba za su kirgu ba, kuma dukkan masu laifuffuka ne da ba mu san iyakarsu ba, don haka kada mu yi sanya; yana da matukar alfanu gare mu da mu zauna mu rubuta dukkan bukatunmu gaba daya a takarda, ya kasance in mun zo yin addu’a sai mu dauko mu karanta su ta haka ba za mu mance da ko daya ba daga cikin bukatunmu.
Ma’auratan da za su dace da Ramadan:
▷ Su ne wadanda suka kulla kyakkyawar niyya game da wannan wata na Ramadan, watau suka yi niyyar yin dukkan ayyukan alheri a cikin wannan wata, kuma suka yi niyyar kyamata da gudun dukkan wani aikin sabo ko shagala, sannan kuma suka tabbatar da wannan niyya cikin zuciyar da tunaninsu.
▷ Su ne wadanda za su yi aiki da kyakkyawar niyyarsu da kudurorinsu da suka yi ba tare da fashi ko gajiyawa ba, tun daga farko har karshen wannan wata mai cike da rahmomi.
▷ Su ne wadanda suke tsara lokutansu na cikin Ramadan gaba dayansa, ya kasance kowace dakika sun kididdige ta sun tanadar mata wani aikin alherin da za su yi a ciki. Sun yi jadawalin yin ibadodi irinsu karatun kur’ani, karantawa ko sauraren tafsiri, yin zikirori daban-daban, yin sallolin nafila, da sauran ayyukan alheri kuma ba su taba tsallekewa ko yin fashin daya daga cikin ayyukan da ke cikin jadawalinsu ba.
▷ Su ne wadanda suka yi sababbin tsare-tsare da canje-canje na alheri, musamman don Ramadan, kamar kawar da duk wasu hotuna daga cikin gidajensu, musamma a wajen da ya kasance ana yawan yin ibada a cikinsa; da cire duk wasu tasoshin fina-finan da na sharholiya daga akwatin satilayit dinsu; kamar kauracewa sauraren wakoki ko maganganun banza a waje da cikin gidajensu; kamar daina kallon fina-finai sai na wa’azi da masu kara inganci a rayuwa da addini. Da cire duk wasu kafar hirarraki da sada zumunci na yanar gizo daga cikin wayoyinsu, (social applications), har sai bayan Ramadan, da nufin karin lokacin kusantar Allah Madaukaki ba tare da wadannan kafafen sun dauke musu hankali ba; da sauran muhimman canje-canje da suka dace irin yanayi da rayuwar ma’aurata.
▷ Su ne wadanda za su dage, wajen kusantar Allah Madaukaki a ciki da ma bayan Ramadan.
▷ Su ne dai wadanda za su dabbakar niyyar barin wani aikin sabo, ko wani halin da bai dace ba a cikin wannan wata. Kamar in uwargida ta san akwai wani abu da take yi wanda ta san maigidanta ba ya sonsa sai ta yi niyyar ba za ta kara aikata wannan abu ba cikin wannan wata da ma bayansa.
Kusantar Allah
Yara
Sa ibada gaba da komai
Kusantar da dukkan kazanta
Tilawah, Tahajjud, Taraweeh, Tasbeehat, Tadharru’ (ferbent Dua), Tatawwu’ (Nafl Ibadah), Tasahhur (eating Sehri / Suhoor), Taubah (repentance), Tawadhu (humility) and Tafakkur (contemplation).
Shawarwari da karin bayani daga masu karatu.
Assalamu alaikum,
Ina ba Ma’aurata shawara su zama masu yawan tsafta da gyara jiki a kodayaushe musamman mata, da haka ne za su zama masu sha’awar juna da kuma so da kauna. Matan aure ina ba ku shawara idan za ku aikata wani abu kowane iri ne, to ku shawarci mijinku, domin idan mace ta yi aure ba ta da wanda ya kai mijinta.
Wani Bawan Allah.
Assalam, karin shawara nake so na ba ma’aurata a kan hakkokin juna, musamman wanda aka yi tarayya a ciki, kamar tsare mutunci da na ibadar aure: yawancin mata suna daukar namiji ne da alhakin gamsar da mace a ibadar aure, ko kuma shi kadai ne aka dora wa hakkin kare mutunci, alal hakika wadannan hakkoki an yi tarayya ne a cikinsu, kada mace ta dauka lallai dole namiji ne zai neme ta da ibadar aure, kuma ya gamsar da ita, ita ma yana da hakki a kanta na ta yi misa duk abin da ya dace don ta tayar masa da sha’awa yadda za su yi ibadar a cikin nishadi da hauhawar sha’awa, ba kawai a yi dan sauke hakki ba. Haka batun yake a wajen kare mutunci, kowa zai yi duk abin da ya dace don kada mutuncin dan uwansa ya tozarta. Da fatan ma’aurata za su dinga neman hanyoyi sababbi domin motsar da sha’awa ba kawai a tsaya a hanya daya ba ta kaka da kakanni.
-Malama Karymatau
Assalam, jan hankalina a kan ma’aurata musamman ’yan uwana mata a kan wani hali na zargi da muke yi wa masu gidanmu a kan yana yin wani abu ga abokiyar zamanmu, mu kuma ba ya mana, ko bai ba mu ba,wanda ba lalle muna da hujja ba, kuma ko ma akwai hujja to tamu nasiha ce kadai, amma idan mu ka yi hakuri Allah ba zai kama mu da wani laifi ba, sai ma ladan hakuri da kuma karin kima a wajen miji, saboda zai ga ba a sa masa ido ba. Idan kuwa muka sa irin wannan zargin to akwai yiwuwar yin laifi, domin in dai ya zama hali to dole mu jefa tsoro a zuciyar maigida, kuma ya dinga ganin bakinmu.
Wata baiwar Allah
Ma’auratan da za su dace da Ramadan
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu bayanan da za su zo cikin sa, amin. In…