Ma’aikatar ayyuka da wutar lantarki da gidaje ta samu kaso mafi tsoka na Naira biliyan 555 da digo 88 na kasafin kudin shekarar 2018.
Cikin Naira tiriliyan takwas da digo 61 na kasafin kudin gwamnati ta ware Naira tiriliyan uku da digo 49 na ayyukan yau da kullum da Naira tiriliyan biyu da digo 41 na manyan ayyuka.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin ga hadin gwiwar majalisar dattawa da ta wakilai jiya.