✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan lafiya sun janye yajin aiki

Hadakar kungiyoyin lafiya wacce a takaice ake kira JOHESU ta janye yajin aikin da ta shiga na kwanaki 13 tare da umartar mebobinta na kasa…

Hadakar kungiyoyin lafiya wacce a takaice ake kira JOHESU ta janye yajin aikin da ta shiga na kwanaki 13 tare da umartar mebobinta na kasa baki daya su koma bakin aiki a yau 5 ga watan Oktoba.
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin, Biobelemoye Josiah, ya ce kungiyar ta sami dukkanin takardun yarjejeniyar da ta yi da gwamnatin tarayya.
Saboda haka ya umarci kungiyoyin da ke karkashin uwar kungiyar JOHESU su kira taro a  yau Laraba su sanar da membobinsu yarjejeniyoyin da aka cimma da gwamnatin tarayya sannan kuma su koma bakin aiki a ranar Alhamis.