✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan ƙananan hukumomi na neman ƙarin kashi 300 na albashi saboda janye tallafin fetur

Bukatar ma’aikatan kananan hukumomin ta ci karo da bukatar uwar kungiyar kwadago ta NLC.

Kungiyar kananan hukumomi ta Najeriya, NULGE ta nemi gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta ƙarawa ma’aikata albashinsu da 300%.

Wannan dai na zuwa ne bayan janye tallafin man fetur, da kuma kara farashinsa a Najeriya da ke ci gaba da janyo martani daga kungiyoyin kwadago a kasar.

Kungiyoyin na hankoron ganin sun sama wa mambobinsu albashin da zai iya rike su a wannan lokaci da rayuwa ta sauya sakamakon tashin farashin komai.

Sai dai a wannan karon a iya cewa bukatar ma’aikatan kananan hukumomin ta ci karo da bukatar uwar kungiyar kwadago ta NLC wadda ta nemi gwamnatin Najeriyar ta yi wa ma’aikata karin kashi 200 domin rage radadin janye tallafin mai.

Cikin sanarwar da NULGE ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Mista Ambali Olatunji, ta ce ta cimma matsaya ne kan karin na kashi 300 bayan taron kolin da ta yi wanda ta ce shi ne ya dace da ma’aikatanta a matsayin mafi karancin albashi.

Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Muhammad Gudaji, ya ce tun da an samu karin da ya fi na kashi 300, amma su sun ce ya kamata a kara musu albashi da kashi 300 a matsayin mafi karancin albashi.

“Shi kansa kaso 300 idan ka duba halin da aka shiga ba wani abu ba ne sai dai shi ma a yi hakuri,” in ji shi.

Ya ce kofarsu a bude take domin tattaunawa da mahukunta don samun maslaha da kuma tsamo jama’a daga halin da suke ciki.

Ya ce a matsayin kananan hukumomin wadanda suka fi kusa da jama’a, sun fi yada arziki a tsakanin al’umma, don haka samun albashi mai kyau a gare su zai taimaka sosai.

“Har yanzu mun san akwai jihohin da ba su ma fara biyan Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi ba don haka wannan karon muna kira da a yi mana,” in ji shi.

Ya ce idan gwamnati ta ki amsa wannan koke nasu za su kira taron mahukunta na gwamnati don tattauna mataki na gaba da ya kamata a dauka.