✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan Kamfanin NNPC sun shiga yajin aiki

kungiyoyin Ma’aikatan mai na Kamfanin NNPC na kasar nan sun shiga yajin aiki don adawa da matakin gwamnati na rarraba kamfanin.kungiyoyin sun kuma rufe duka…

kungiyoyin Ma’aikatan mai na Kamfanin NNPC na kasar nan sun shiga yajin aiki don adawa da matakin gwamnati na rarraba kamfanin.
kungiyoyin sun kuma rufe duka ofisoshin NNPC da ke fadin kasar a shekaranjiya Laraba, kamar yadda BBC ta bayyana.
kungiyar ta ce Shugaban NNPC Emmanuel Ibe Kachikwu bai shawarci masu ruwa da tsaki a kan batun gabanin daukar matakin, inda suka yi zargin cewa Mista Ibe, bai bi ka’ida.
A ranar Talata ne dai Mista Kachikwu ya sanar da raba kamfanin zuwa kafanoni bakwai bayan samun amincewar Shugabn kasa Muhammadu Buhari. An raba kamfanin ne zuwa kamfanoni bakwai inda ko wane bangare ke da shugaba.
Sai dai a yanzu babu tabbas ko yajin aiki zai shafi ayyukan hako danyen mai a yankin Neja-Delta.
Akwai fargabar cewa wannan yajin aikin zai iya jawo karancin man fetur da ake fuskanta a wasu sassan Najeriya.
Bisa sabon tsarin kamfanin, Bello Rabiu shi ne zai shugabanci kamfanin Upstream, wanda ke kula da rijiyoyin mai na kasa da kuma binciko in da akwai yiwuwar za a iya samun danyen mai.
Henry Ikem-Oniy shi ma zai shugabanci Downstream, kamfanin da ke kula da rijiyoyin mai na cikin teku, sai Saidu Mohammed wanda zai jagoranci kamfanin kula da Isakar gas da Lantarki, Anibor Kragha, shine shugaban kamfanin kula da matatun mai na kasa, sai Babatunde Adeniran da zai shugabanci kamfanin kasuwanci, sai Isiaka Abdulrazak da zai shugabanci kamfanin tsare-tsaren ayyuka da kudin na kamfanonin.
Mista kachikwu ya ce sabbin kamfanonin za su mayar da hankali ne kawai kan kasuwanci kamar yadda sauran kamfanonin mai na duniya suke yi.