Kungiyar Ma’aikatan Jiragen Sama ta Najeriya (ANAP) ta yi barazanar fita yajin aiki hadi da zanga-zanga a ranar 26 da 27 ga watan Yuli, don nuna goyon bayanta ga yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU).
Cikin wata sanarwa da Babban Sakatarenta na kasa, Abdulrasaq Sa’idu ya fitar a ranar litinin, kungiyar ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kawo karshen yajin aikin malaman jami’ar cikin gaggawa.
- Shugaban Ukraine ya kori manyan Hafsoshin tsaron kasar 2 saboda ‘hadin baki’ da Rasha
- An zabi Kwamishina a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Oyo
Ya ce yajin aikin kungiyar ba abin da ya haifar ga kasar nan face munanan dabi’u ga daliban matasa da ba su da abin yi, wadanda hakan ka iya zamowa barazana ga rayuwarsu a gaba.
Haka kuma sanarwar ta ANAP ta ce yajin aikin na nuna mawuyacin halin da bangaren ilimin Najeriya ke ciki, wanda hakan abin kunya ne ga shugabanninta.
“Yanzu fa ana maganar shafe watanni hudu ana yajin aikin, kawai saboda gwamnati ta yi kememe ta ki cika alkawarin da ta dauka, ya kamata a ce ta kawo karshensa, da ma na kungiyoyin NASU, da SAUTHRIAI, har ma da NAAT.”
Haka kuma Kungiyar ta ce yajin aikin ba fa wai iya ‘ya’yan kungiyar ASUU ke wahala saboda shi ba, har ma da iyaye da al’umma, ban da matsalar tattalin arzikin kasar da ya leka kowanne gida.
Haka kuma ANAP ta ce ilimi jigon ci gaban kowacce al’umma ne, wanda ke kai ta ga babban mataki a idon sauran kasashen duniya, kuma yin shakulatin bangaro da lamarinsa abu ne da za a yi da na sani kan sa a gaba.
“‘Ya’yan mu na shafe shekara takwas madadin hudu da ya kamata ace sun yi a jami’o’i, lamarin fa ba zai yiwu a haka ba, don haka za mu hada hannu da kungiyar kwadago domin fara namu yajin aikin,” inji sanarwar.