Kungiyar Manyan Ma’aikatan Asibitocin Koyarwa da Cibiyoyin Bincike (SSAUTHRIAI) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako guda ta biya mambobinta bashin alawus-alawus din da suke bin ta.
Sanarwar hakan na cikin bayanin da kungiyar ta fitar ta hannun mukaddashin shugabanta, Malam Kabir Mustapha da sakataren riko, Mista Joseph Ugwoke, bayan taron yini biyu da kungiyar ta gudanar.
Kungiyar ta ce ba lallai ne mamabobinta su ci gaba da zuwa aiki ba muddin gwamnati ba ta biya su dukkan hakkokinsu a cikin mako daya ba.
Don haka ta nusar da gwamnatin bukatar da ke akwai na ta biya bukatunsu don kauce wa tilasta mata shiga yajin aiki.
Ta ce ta rubuta wa gwamnati takarda sau sa da dama don yi mata tuni, amma duk da haka gwamnatin ta yi biris.
Ta kuma nuna damuwarta kan yadda gwamnatin ta ware likitoci ta biya su ba tare da ta biya sauran ma’aikatan ba.