✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ma’aikata sun garkame majalisun dokokin Yobe da Jigawa

Ya kuma sha alwashin cewa za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar har sai lokacin da Gwamnatain Tarayya ta amince ta biya musu bukatun…

Mambobin Kungiyar Ma’aikatan Majalisun Dokoki ta Najeriya (PASAN) a ranar Talata sun garkame ginin Majalisar Dokokin Jihar Yobe bisa neman a basu damar cin gashin kansu a bangaren kudade.

Da ya jagoranci masu zanga-zangar a harabar Majalisar dake Damaturu, shugaban kungiyar, Kwamared Zanna Ali ya ce sun yanke shawarar hana ruwa gudu a majalisar har sai an biya musu bukatunsu.

Ya ce zanga-zangar wani mataki ne na bin umarnin uwar kungiyar ta kasa na shiga yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya.

Kwamared Zanna ya ce sun dauki matakin ne don su nuna kin amincewarsu kan rashin aiwatar da ’yancin cin gashin kai ga majalisun jihohi da bangaren shari’a kamar yadda doka ta tanadar.

Ma’aikatan Majalisar Yobe yayin zanga-zangarsu a Damaturu

A jihar Jigawa ma, mambobin kungiyar ta PASAN sun yi wa gignin Majalisar Dokokin Jihar kaka-gida tare da tsayar da komai cik.

Tun da farko da yake jawabi a harabar majalisar ranar Litinin, shugaban kungiyar reshen jihar ta Jigawa, Malam Umar Kazaure ya ce matakin da suka dauka ya biyo bayan karewar wa’adin da suka ba Gwamnatin Tarayya na kwanaki 21 ne kan aiwatar da dokar wacce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu kimanin shekaru biyu da suka gabata.

Ya ce hakurin ma’aikatan majalisun ya kare, kuma kamata ya yi a biya su hakkokinsu kamar yadda doka ta tanada.

Ya kuma sha alwashin cewa za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar har sai lokacin da Gwamnatain Tarayya ta amince ta biya musu bukatun nasu.