Wata ma’aikaciya a Sashin Bincike da Nazari a Kamfanin Media Trust Limited, mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Abuja, Rabiyat Usman ta yi zarra, inda ta zo ta daya a gasar da Kamfanin LeadrCom yake shiryawa duk shekara.
Kamfanin LeadCom ya kasance mai bayar da jagora da kwarin gwiwa ga matasa wajen fahimtar irin baiwar da Allah Ya yi musu ta fikira da kirkira da kuma koya musu dabarun shugabanci a fannonin rayuwa daban-daban. Kamfanin yana tattara matasa daga sassan Najeriya duk shekara domin koyar da su wadannan dabarun, inda daga bisani ake zaben wanda ya fi nuna kwazo da fikira a matsayin zakara.
Maudu’in LeaderCom na bana shi ne “Labarin Rayuwata, Labarina na Gaskiya,” inda kwararrun malamai 11 suka koyar da matasa 27 dubarun shugabanci a fannoni daban-daban na rayuwa, kuma daga bisani suka fafata gasa a tsakaninsu dangane da abin da suka koya.
Rabiyat wacce ta kasance hazika, ta kammala digirinta na farko a fannin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Aba da ke Jihar Abiya, inda ta samu kyakkyawan sakamako na Digiri Mai daraja ta Daya (First Class). A wannan gasa kuma, ita ce ta yi wa mutum 12 zarra, wadanda aka tace daga cikin mutum 27 da suka fafata a gasar.
Wata matashiya mai suna Atuzie Tuzzi, Manajar Kamfanin TRT-Ebents ce ta zo ta biyu; yayin da Nendimwa Malafa ta Kamfanin Yali-Network da ke Legas ta zo ta uku.
Gasar wacce aka gudanar da ita a tsawon kwana biyar a Legas, wasu kungiyoyin sa-kai ne biyu, SerbeLead Global da Social Good Fund suka dauki nauyin shirya ta.
A yayin da take hira da manema labarai lokacin da aka mika mata kambi, Rabiyat ta ce lokaci ya yi da matasa za su rika mai da hankali wajen sassan da za su inganta musu rayuwa a yayin da suke tu’ammali da shafukan sada zumunta na Intanet. Ta shawarce su da su rika zurfafa iliminsu musamman ta fannin kirkire-kirkire ta amfani da Intanet, maimakon bata lokaci wajen surutai da sharholiya.
“Ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta, za ka samu damar bayyana ra’ayinka da hikimominka ga al’ummar duniya,” inji Rabiyat.
“Don haka a duk lokacin da mutum ya samu dama, to ya bayyana fasaharsa da hikimarsa ga al’umma yadda zai fadakar da su kuma ya amfane su da wani abu da ya sani, yadda mutane za su fahimta sosai. Mu yi duk abin da za mu yi mai amfani domin kyautata kasarmu Najeriya. Kuma wannan bai tsaya ga matasa kadai ba, a’a, kowa zai iya shiga kafar sada zumunta ta Intanet ya ba da gudumawar wani abu da ya sani da zai taimaki al’ummar duniya gaba daya,” inji ta.