✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikacin da ya shafe shekara 84 yana aiki a kamfani daya

Ya fara aiki da kamfanin ne tun a 1938

Wani ma’aikaci mai suna Walter Orthmann, mai shekara 100 dan kasar Brazil ya shafe shekara 84 yana aiki a kamfani daya.

Ya fara aiki da kamfanin ne tun a 1938, wanda a hukumance ya sa aikinsa ya cancanci shiga Littafin Kundin Tarihi na Duniya (Guinness Book of Records).

Orthman ya fara aiki da Kamfanin Industrias Renaux SA, wanda kamfanin masaku ne a garin Brusque da ke kasar
Brazil, a ranar 17 ga Janairun 1938, lokacin yana dan shekara 15 kacal.

Ya fara ne a matsayin mataimaki a sashen jigilar kayayyaki, amma a tsawon shekaru, an kara masa girma zuwa mataimaki mai gudanarwa kuma a karshe ya samu ci gaba zuwa Manajan Tallace-Tallace.

A cikin shekara 84 na aikinsa, Walter ya yi tafiye-tafiyen tallace-tallace a duk fadin duniya, yana karbar kudinsa a cikin nau’o’in kudi daban-daban guda tara, kuma ya yi amfani da kusan kowane irin jirgin sama wajen kasuwanci a tarihin jiragen sama na Brazil.

“Dole ne ku so yin aiki. Na fara aiki da sha’awa da ruhin shahara,” inji Walter Orthmann, lokacin da aka tambaye shi abin da ya sa ya ci gaba da aiki sama da shekara 80.

“Ba za ku iya yin aiki kawai, don ku ce kuna aiki ba. Wannan ba ya da manufa.Ba za ku iya jure wa hakan ba,”
inji shi.

A watan Fabrairun bana, sunan Walter Orthmann ya samu shiga cikin Kundin Tarihi na Duniya saboda samun lambar yabo ta mafi tsawon lokaci yana aiki a kamfani daya (shekara 84 da kwana 9).

A ranar 19 ga Afrilu, ya cika shekara 100, amma ba ya da shirin yin ritaya daga kamfani daya tilo da ya yi wa aiki.

Da yake tunawa da farkon aikinsa a Kamfanin Industrias Renaux S.A. (Kamfanin RenauxView), Orthmann ya ce, babu kwamfutoci, ba a yin amfani da wayoyi a kamfanin, kuma dole ne a buga rubutu a keken tafiraita (typewriter).

“Babu fitilun lantarki a gari, tituna a kazance, ana fama da tavo a duk lokacin da aka yi ruwan sama a hanyoyi. Babu
ruwan famfo, kuma kowane gida yana da rijiyarsa.

“Komai ya fi sauki a yau, Orthman ya yarda da hakan. Duk abin da kuke bukata shi ne wayar hannu da Intanet, kuma kuna iya daidaita kasuwanci daga ko’ina cikin duniya.

“Godiya ga fasahar da take iya saukaka ci gaban aiki, kamar yadda yake a shekarun bayan nan,” inji shi.

Da aka tambaye shi ko wace shawara zai bai wa mutanen da suke mafarkin ci gaba da kwazo da yin aiki a karshen rayuwarsu? Orthman ya bayyana wa shafin Intanet Globo na Brazil cewa: “Kada ku yi fushi, ku yi komai kuna dariya. Kawai ku yi abin da kuke son yi. Ina son yin aiki a wannan kamfanin. Kada ku samu abokan gaba. Ku yi hakuri.

Ku kasance cikin natsuwa. Rayuwa hanya ce kawai a nan duniya, ku ji dadinta, ku yi abin da kuke so.”