✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ma’aikacin Aminiya Ya Lashe Lambar Yabo kan Rikon Amana

Sani Ibrahim Paki, ya lashe Lambar Yabo kan Tsare Gaskiya na Rikon Gaskiya a wurin gudanar da aiki

Ma’aikacin Aminiya, Sani Ibrahim Paki, ya lashe Lambar Yabo kan Tsare Gaskiya da Rikon Amana a yayin gudanar da aiki.

An karrama Sani Paki, wanda ke aiki a sashen yada labarai ta intanet na Aminiya ne a wani kasaitaccen biki, tare da sauran takwararinsa Hamza Adamu, saboda yadda suka yi zarra wajen rikon amana.

Kazalika an karramma Abdulaziz Abdulaziz, Mataimakin Janar Edita na Jaridar Daily Trust da kuma Gaza Yakubu na Trust TV, wadanda su kuma kowannensu ya samu lambar yabo kan nagartar aiki.

Bikin da aka gudanar a ranar Laraba da dare, ya kuma karrama ma’aikata da suka shekara 20, 15 da kuma kuma suna aiki a Rukunin Kamfanin Yada Labarai na Media, masu wallafa jaridun Daily Trust, Aminiya, Trsut TV.

Karo na 12 ke nan da kamfanin yada labaran ya gudanar da irin wannan biki domin kara wa ma’aikatansa kaimi da kuma yaba wa wadanda suka dade suna hidimta masa da kuma wadanda suka nuna bajinta.

Sauran wadana suka lashe kyautar sun hada da Abdulaziz Abdulaziz, Mataimakin Janar Edita na Jaridar Daily Trust da kuma Gaza Yakubu na Trust TV, wadanda su kuma aka karrama da lambar yabo kan nagartar aiki.

Mutum biyu daga cikin ma’aikatan, Yusha’u Adamu da Ibrahim da Usman Ja’afaru sun samu lambar yabo kan shafe shekara 20 suna aiki da kamfanin, sai wasu bakwai da suka shafe shekara bakwai.

Wadanda suka shekara 15 su ne Isiaka Wakili, Abbas Jimoh, Aminu Nasidi, Abdullahi Ammani, Fidelis Macleva, John Anyimbe Ayim da kuma Simon Ekankang.

Akwai kuma wasu mutum 39 da suka cika shekara 10 da aiki a kamfanin, daga bangaren yada labarai, sashen samar da tsaro, sashen kula da ma’aikata, sashen kasuwanci da tallace-tallace da sauransu.